Korona: Iran Ta Kulle Iyakokinta Da Iraqi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Umar Shu’aibu
Kasar Iran ta sanya dokar hana zirga-zirgan Fasinjoji a iyakoki Biyar dake tsakanin ta da kasar Iraqi saboda dakile cigaban yaduwar sabuwar nau’in Cutar Korona.

A yau Litinin 22 ga watan Fabrairu 2021 ofishin Kwatsam na Iran suka fitar da sanarwar dakatar da shige-da fice a iyakoki Hudu dake tsakanin kasar da Iraqi, karin iyaka na Biyar kuma za a kulle shi zuwa gobe Talata.

Kakakin Hukumar Rouhullah Latifi yace an dau matakin ne domin dakile cigaban yaɗuwar sabuwar nau’in cutar Korona saboda rahotanni da aka samu na saurin yaɗuwar cutar a Lardunan Kasar dake kan iyakokin Kasashen biyu.

Latifi ya kara da cewa dokar zata shafi dukkan matafiya ne harda masu izinin tafiya na musamman da ma’aikatan Diflomasiyya.

Rahotanni sun nuna cewa iyakokin zasu cigaba da zama a garkame na tsawon sati biyu.

Kasar Iran na kokarin kare karo na huɗu na yaduwar cutar Korona gabannin bukukuwan sabuwar Shekarar Shamsiya da za a fara a karshen watan Maris 2021.

A kwanakin baya Hukumomin Lafiya na Lardin Khuzistan dake Kudu maso yammacin Kasar suka tabbatar da shigowar sabuwar nau’in cutar ta Korona.

Adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a kasar Iran sun kai miliyan 1.5 yayin da adadin ‘yan kasar da suka mutu a sanadiyar cutar suka kai kimanin dubu 60. Kasar ta fara shirin riga-kafin cutar ga ma’aikatan lafiya dake sahun gaba wurin kula da masu cutar a farkon wannan watan da muke ciki.

A yau Litinin Kakakin Ministan harkokin kasashen wajen kasar ya bayyana cewar wani rukuni na riga-kafin cutar Korona samfurin Sinopharm da kasar China ta baiwa Kasar Iran na gab da isowa kasar.

Share.

About Author

Leave A Reply