Kafa Dokar Hana Cin Ganda Zai Bunkasa Masana’antu Da Samar Da Aikin Yi Ga ‘Yan Nijeriya–Farfesa M K Yakubu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Bello Hamza

Shugaban Cibiyar Kimiyyar Fasahar Sarrafa Fatu ta kasa (NILEST) da ke Zariya a Jihar Kaduna Farfesa M K Yakubu Koko ya bayyana cewa, in har aka samu nasarar kafa dokar hana cin fatun dabbobi da sunan ganda hakan zai taimaka wajen bunkasa masa’anantumu da kuma samar da aikin yi ga dinbin matasan kasar nan. Farfesa Yakubu ya bayyana hakja ne a tattaunawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Zariya a karshen mako.

Ya ce, wanann shawarar ya fito ne sakamakon tattaunawa da masu ruwa da tsaki suka yi da kuma lura da tanafde tanaden Shirin kas ana bunkasa harkokin masana’antun sarrafa fatu na kasa (national Leather policy). Wannan matakin zai kai ga samar da isasshe fatu ga masana’antun mu na masu saffara fatu wadanda suka dukrkeshe samakamon rashin isassun fatu.

A saboda haka ya nemi hadin al’umma don samun nasarar wannan tsarin wanda aked sda ran zai kai ga samarwa dinbin matasanmu aikin yi, mudsamman ganin a halion yan zunzu samun aikin gwamnati yana da matukar wahala.

Hakanan Farfesan ya yi takaici yadda a wannan kasarce kawai aka fi cin fatar dabbobi a cikin jerin kasashen duniya, wanda ko a kimiyance fata bata kara komai a cikin jikin Dan adam, maimakon haka kuma tana cutar da mutane ta hanyar haifar da cutar kansa.

Hakanan ya ce matukar aka samar da wannan doka zai iya dawo da martabar Kamfanonin sarrafa fatun kasarnan kusan 45 da ake da su a fadin kasar nan wanda kuma a lokaci guda za su iya samar da aikin yi ga yan kasa da dama.

Daga karshe Farfesan ya bada hakuri musamman ga mutanen da suke tu’ammuli ta hányar ci da sana’ar  fatan ganin cewar sana’ar tasu za ta iya nakasa, saidai ya dauki alwashin samar da daidaito a tsakanin cibiyoyi da Kamfanoin sarrafa fata dake kasarnan.

Share.

About Author

Leave A Reply