Abin Tausayi: An Yi Wa Wani Mutum Bulala Kan Satan Gero Mudu 9 A Jigawa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +
  1. Wata kotun Shari’a da ke Dutse a Jigawa ranar Talata ta yi umurnin a yi wani Abdullahi Ya’u mai shekara 20 bulala biyar kan satar mudu 9 na gero.

Ya’u, wanda mazaunin kauyen Bakin Jeji ne na karamar hukumar Dutse, ya gurfana gaban kotun don fuskantar tuhumar tsallake da sata.

Mai shari’a Muhammad Adamu, ya hukunta Ya’u ne bayan ya amsa laifinsa.

Adamu ya yanke wa wanda ake zargin hukuncin daurin wata biyar da zabin biyan naira 3,000.

Wanda aka hukuntan ya biya 3,000.

Kafin nan, mai karanto karar, Sufeto AbdusSalam Baraya, ya bayyana wa kotun cewa wani Ya’u Alhaji ne ya kawo karar ofishin ‘yan sanda na Fanisau a Dutse ranar 8 ga watan Satumba.

Baraya ya ce ya wanda aka hukuntan ya saci mudu tara na gero daga gidan wanda ya kawo karar.

Ya ce laifin ya saba wa sashe na 183 da 148 na Dokokin shari’a na Arewa na 2012.

 

Share.

About Author

Leave A Reply