Albashin Malaman Jami’a: Zuwa Ga Shugaba Buhari!, Daga Farfesa Ibrahim Malumfashi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Barka da shan ruwa, da kuma fatar Allah ya amshi ibadarmu a wannan wata mai alfarma, amin ya Allah!

Na rubuto wannan gajeruwar wasika ne domin na yi maka tuni game da albashin MALAMAN JAMI’A da gwamnati ta rike na kusan tsawon wata 4.

Ya mai girma Shugaban Kasa, kwanakin baya ka umurci da a biya Malaman Jami’ar albashinsu na watan FABRAIRU da MARIS, musamman ganin halin da kasar nan take ciki na annoba da rashin kudi da abinci ga al’umma ga kuma zaman gida.

Ya Shugaba Buhari, ina sanar da kai cewa har zuwa yau ba a biya wadannan bayin Allah hakkinsu ba, duk da umurnin da ka bayar, ga shi mun shiga wata na HUDU ke nan, AFRILU da MAYU!

Na san kila ba ka san cewa ba a kaddamar da wannan umurnin naka ba, shi ya sa, Idan kuma kana sane, ka dai janye umurnin na biyan wadannan bayin Allah hakkinsu ne, don Allah ka fada, mu sani domin nu ci gaba da hakuri yadda muka saba.

Ina jiran amsa ko da ta hannun Bashir Ahmad ne ko kuma ta wajen @femiadesina ko Garba Shehu ko wani makusanci da zai iya kai wannan koke gare ka!

Na gode

Ibrahim Malumfashi

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply