Obobo: Dan Nijeriyan Da Zai Je Saudiyya A Keke Ya Bar Nijar

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rahotannin da ke shigo wa Jaridar Tantabara Hausa shi ne, wannan matashin dan Nijeriya mai suna Ali Obobo ya isa kasar Nijar a kudurinsa na son zuwa Saudiyya.

Shi dai wannan matashi ya tashi ne daga garin Jos na Jihar Filato a farkon makon Maris din wannan shekara.

A yau lahadi ne misalin karfe 12:00 na rana matafiyin ya isa kauyen Kinchandi ta Jihar Diffa wanda daga nan zai fice daga Nijar.

Har yanzu dai ana ci gaba da tantamar yadda wannan bawan Allah zai samu shiga Saudiyya a wannan yanayi na annobar #Coronavirus.

Share.

About Author

Leave A Reply