Al’ummar Jihar Katsina Sun Yaba Wa Buhari Kan Samar Da Hanyar Jirgi Daga Katsina Zuwa Maradi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Al’ummar jihar Katsina sun yaba wa gwamnatin tarayya akan aikin samar hanyar jirgi daga Kano zuwa garin Maradi da ke jamhuriyyar Nijar.

Wasu da manema labarai suka tattauana da su a wurare daban daban sun bayyana cewa, samar da hanyar jirgin zai taimaka wajen bunkasa harkokin tattalin arzuki na kasashen biyu.

Malam Hamisu Lawal, wani mazaunin garin Daura, ya muna farin cikinsa akan sa hannun akan kwangilar da aka yin a samar da hanyar jirgin kasar.

Lawal, ya kuma kara da cewa, wannan shi ne karon farko da aka samar da irin wannan aikin ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya kan shirin aikin.

Ya kuma ce, al’ummar yankin garuruwan Daura, Mashi and Jibia a jihar Katsina, da kuma garuruwan Danbatta a jihar Kano da kuma garin Kazaure a jihar Jigawa za su amfana da aikin da.

Ya kuma kara da cewa, shirin za taimaka wajen rage talauci a yankunan.

Ya kuma bukaci gwamnati ta tabbata da an kammala akin akan lokaci don al’umma su amfana da shi.

Share.

About Author

Leave A Reply