An Bukaci Musulmi Su Yi Shirin Fuskantar Azumin Ramadan

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wani malamin addinin musulunci mazaunin garin Ilorin ta jihar Kwara, Farfesa Abubakar Ali-Agan, ya bukaci al’umma Musulmi da su tashi tsaye wajen shiya fuskantar watan azumi mai kamawa, ta hanyar tsayar da dokokin adinin musulunci don ta haka ne za a samu cimma dukkan ladan da ke tattare da watan.

Farfesa Ali-Agan, ya bayar da wannan shawarar ne a hudubarsa ta Juma’a a masallacin Madrasat-Muhammad ranar Juma’a, ya ce, dokokin addinin musulunci ne ke tafiyar da rayuwar dukkan musulmi a kowanne lokaci.

Shikashikan musulunci sun hada da kalmar shahada da sallah da zakka da kuma azumi sai zuwa hajji ga wanda yake da hali.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa a kan yadda wasu musulmi ke wasa da dokokin addini a rayuwarsu.

Ya kuma kara da cewa, addnin musulunci nada dukkan dokokin da ya kamata a bi a rayuwar mutum, akan haka ya kamata musulmi ya bi dokokin musamman a cikin wannan watan na Ramadan mai kamawa.

Ya kuma yi addu’a Allah ya bamu ikon gudanar da bauta yadda ya kamata a cikn watan na Ramadan don mu samu cikakken ladan da ake samu.

Share.

About Author

Leave A Reply