An Daura Aure 1,040 A Karamar Hukumar AMAC A Cikin Wata 6

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

An samu nasarar daura aure  fiye da 1,040 a karamar hukumar AMAC da ke yankin babbar birnin tarayya Abuja a cikin wata 6 da suka gabata.

Mr Akinwumi Akintayo, babbar rajista a karamar hukumar ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja ranar Laraba.

Akintayo ya kuma kara da cewa, a daidai lokacin da ke magana an samu nasarar ceto wasu aure 7 da sua kusa mutuwa ana yi sulhu a tsakanin ma’auratan.

”Yin sulhu a tsakanin iyalan wani babbar nasara ce da karamar hukmar ta samu a wanan lokacin.

“Muna kuma cigaba da kokarin yin sulhu a tsakanin ma’aurata da dama a yankin, akan haka muke kira ga ma’aurata dasu kasance masu hakuri da neman fahintar juna don yadda aure ke mutuwa a fadin kasar nan ke mutuwa abin yana da ban tsoro.

Ya kuma shawarci masu shirin aure dasu tabbatar da soyayya a tsakaninsu kafin su fada auren.

 

Share.

About Author

Leave A Reply