An Gufanar Da Abokai 4 A Kotu Bisa Zargin Lalata Kantangar Wani Gida A Legas

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Talata ne aka gurfanar da wasu abokai 4 a gaban Kotun majastare da ke Ikorodu Legas bisa zargin rusa katangan wani gida tare da kuma satar rodin gini da aka kiyasta kuin su ya kai Naira Miliyan 3.5.

 

‘Yan sanda sun gurfanar da Oyenuga Wasiu, mai shekaru 52; Yekinni Fatai, 32; Oteniya Kazeem, 50; da Salau Olayinka, 39; wanda ba a bayar da adiresoshinsu ba, tare da hadin baki, aikata laifi da kuma lalata dukiya da ganganci.

 

Wadanda ake zagin sun musanta laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

 

Lauya mai shigar da kara, Insp Adegeshin Famuyiwa, ya bayyana wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 29 ga Disamba, 2020 da misalin karfe 9 na safe a yankin gonar Jerry na Ikorodu.

 

Famuyiwa ya yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun kutsa kai cikin wani fili mallakar Olayinka Owoeye kuma sun saci sandunan rodin karafa da kudinsu ya kai Naira miliyan 3.5 da kuma kwanon rufin da kudinsu ya kai N800,000.

 

Ta ce laifin ya sabawa sashi na 411, 52, 350 da 281 na dokar masu laifi na jihar Legas, 2015.

 

Alkalin kotun B.A. Sonuga, ya bayar da belin wadanda ake zargin a kan kudi N500, 000 kowannensu.

 

Share.

About Author

Leave A Reply