An Gurfamar Da Dan Achaba A Kotu Saboda Laifin Zamba Cikin Aminci

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Alhamis ne aka gurfanar da wani dan achaba mai suna Mohammed Sani dan shekara 32 a gaban kotun majastare da ke Kaduna saboda zarginsa da aka yi masa na zamba cikin aminci da kuma cuta.

Mohammed Sani, wanda mazaunin Ungwan Sarki a Kaduna ne, yana fuskantar tuhuma ne kashi biyu da suka hada da zamba cikn aminci da kuma cuta.

Mai gabatar da karar, Insp. Chidi Leo, ya bayyana wa kotun cewa, wani ne mami suna Umar Kabiru ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Gabasawa a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Ya kuma ce, a watan Oktoba 2020, wanda ake zargin ya karbi mashin kira Bajaj da aka kiyasta kudinta ya kai N210,000 da nufin yin  achaba yana kuma kawo balance na N1, 000 a kullum. Amma bayan da ya karbi mashin din sai aka neme shi aka rasa sai a ranar 28 ga watan Fabrairu aka samu nasarar kama shi.

Mai gabatar da karar ya kuma ce, da aka kama shi sai ya bayyana cewa, ya ba wani ne mai suna Shehu Abdullahi wanda kuma zuwa yanzu ba a san inda yake a matsayin jingina.

Ya kuma ce laifin ya saba wa sashi na 234 da 241 na dokokin Fanel lot na jihar Kaduna na shekarat 2017.

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da aka karanto masa jerin laiffukan.

Daga nan ne alkalin kotun Ibrahim Emmanuel, ya bayar da belin wanda ake zargin akan N150, 000 tare da kawo mutum daya da zai tsaya masa. Ya kuma daga karar zuwa ranar 25 ga watan Maris don gabatar da shaidu.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply