An Gurfanar Da Fasto A Kotu Kan Yi Wa ‘Yar Shekara Tara Fyade

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wani fasto mai shekara 38, Idowu Samson, ranar Litinin ya gurfana gaban wata kotun Majistare da ke Iseyin kan zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara tara.

Mai karanto karar, Sufeto Shaib Shedrack, ya bayyana wa kotun cewa wanda ake zargin na da coci ne a garin Iseyin, kuma ya aikata laifin ne ranar 19 ga watan Agusta.

“Ya sanya yatsa a farjinta ne, kan cewa zai cire mata shaidunan da ke cikin jikinta.

“A nan ya yi amfani da ita, kafin jama’a su zo cocin.

“Ya yi wa iyayen yarin karya cewa zai wanke mata shaidunan da ke jikinta ne,” kamar yadda Shaib Shedrack ya bayyana wa kotun.

Ya ce laifin ya saba wa sashe na 210 (A) Cap C38 na Dokokin tarayya na shekarar 2004.

Sai dai, ya musanta zargin da ake masa.

Lauyan wanda ake kara, Ade Bamgbose, ya nemi a bai wa wanda ya ke karewa beli.

Mai shari’a, Maaruff Mudashiru, ya yi umurnin ajiye wanda ake zargin a fursuna kafin ya yanke hukunci kan belin.

Daga nan, Maaruff Mudashiru, ya sanya ranar 12 ga watan Oktoba don sauraron hukuncinsa kan belin.

 

Share.

About Author

Leave A Reply