An Gurfanar Da Wani Dan Kasuwa Bisa Laifin Damfara A Kaduna

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Talata ne aka gurfanar da wani mai suna Gabriel James mai shekara 38 a duniya a gaban kotun majastare da ke Kaduna bisa lafin damfarar Naira Miliyan 1.2.

James wanda ya ke zaune a unguwan Down Quarters, Kakuri, Kaduna, yana fuskantar tuhumar cuta ne da kuma yin sojan gona.

Dan sanda mai gabatar da kara, Chidi Leo, ya bayyana wa kotun cewa, wata mai suna Esther Abraham na unguwar Kinkinau, Kaduna, ta kai rahoto a ofishin ‘yan sanda da ke Gabasawa Kaduna a ranar 15 ga watan Disamba 2020.

Ya kuma kara da cewa, a watan Satumba ne na shekarar 2020, wanda ake zargin ya sayar wa mai karar da fili a Ungwan Makama kan hanyar Yakowa a garin Kaduna, akan Naira Miliyan 1.2.

“Wanda ake zargin ya karbe kudaden mai karar ya kuma bata takardar filin na bogi,’’ inji shi.

Mai gabatar da karar ya kuma duk kokarin da aka yi na karbo kudadedn ya ci tura.

Ya kuma ce laifin ya saba wa shashi na 344 da 138 na dokar fanel kot na jihar Kaduna na shakarar 2017.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifin akan haka ne alkalin kotun Ibrahim Emmanuel, ya bayar da beli shi, ya kuma daga karar zuwa ranar 28 ga watan Janairu don kawo shaidu.

Share.

About Author

Leave A Reply