An Gurfanar Da Wata Mata Da Danta A Kotu Bisa Zargin Satar Mashin A Jihar Osun

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

An gurfanar da wata mata mai suna Patience Ayube mai shekara 52 a duniya tare da danta mai suna Josiah a gaban kotun majastare na garin Ile-Ife, ta jihar Osun bisa zargin satar mashin da aka kiyasata kudinshi ya kai Naira 285, 000.

Haka kuma ‘yan sanda na tuhumar Ayube, da Oluwaseun Joseph, da kuma Friday Emmanuel, da laifin hada baki da kuma taimaka wajen satar mashin din.

Mai gabatar da karar, ASP Abdullahi Emmanuel, ya bayyana wa kotun cewa, wadanda ake zargin sun saci mashin ne kirar Honda da aka kiyasta kudinta ya kai N285,000, wanda mallakin wani ne mai suna Emmanuel Akpan.

Ya kuma ce, wadanda ake zargin sun kuma tayar da hankalin al’umma a yakin Texaxo na garin Ile-Ife a yayin da suka je satar mashin din.

Mai gabatar da karar ya kuma ce, laifin ya saba wa sashi na 249(d), 390(9) da 516 na dokokin manyan laifukkan na jihar Osun, na shekarar 2002.

Lauyan wadanda ake karar, Mr Olalekan Babatunde, ya nemai kotu da bayar da belin wadanda ake zargin kamar yadda doka ta tanada.

Alkalin kotun, A.I Oyebadejo ya amince da bayar da beli wadanda ake zargin akan kudi N50,000 kowannen su, ya kuma daga karar zuwa ranar 30 ga watan Yuni don cigaba da karbar shaidu.

 

Share.

About Author

Leave A Reply