An Kaddamar Da Litattafai Uku Da Dakta Yusuf Bala Usman Ya Rubuta Shekara 15 Da Rasuwarsa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Bello Hamza

A dai dai lokacin da ake juyayin cika shekara 15 da rasuwar Dakta Yusuf Bala Usman (ya rasu ranar 24 ga wata Satumba 2005), Malamin Jami’a, kuma masanin tarihi da siyasa. Ya kuma kasance daya daga cikin manyan Malamai masana tarihi da suka yi fice wajen tattarawa tare da taskacewa da yi wa kuma tarihin Nijeriya garambawul. Tuni kuma aminai da abokan aikinsa tare da iyalansa suka kafa cibiya na musamman da ake kafa don tattara tare da taskace ayyukansa da kuma cigaba da gudanar da bincike a kan harkokin tattaliin arzikin al’ummar Nijeriya da kuma na zamantakewarsu mai suna Yusufu Bala Usman Institute a Zariya a shekara 2019.

Cikin ayyukan farko da cibiyar ta fara gabatar wa sun gada da sake wallafa shaharrun littatafan da marigayi Dakta Yusufu Bala Usman ya rubuta a lokacin rayuwarsa, littafatn sun kuma haxa da ‘Nigeria Against the IMF’ da For The Liberation Of Nigeria’ da kuma The Manipulation Of Religion In Nigeria 1977- 1987’. Duk da cewan an wallafa littafan shekaru da dama da suka wuce amma har yanzu tasirinsu na nan, suna kuma kan gaba a halin yanzu a matsayin daftari na warware matsalolin tattalin arziki da na zamantakewar al’ummar Nijeiya haka kuma littafan nada matuqar tasiri a kokarin magance matsalolin tsaro da ke fuskantar sassan qasar nan.

Wannan kuma ba abin makaki bane in aka lura da haziqan masana da cibiyar ta tara a matsayin jagororinta, waxanda suka haxa da Dakta Olusegun Osoba (Shugaba), Norma Perchonock, Farfesa Gideon S. Tseja, Attahiru Bala Usman, Farfesa Usman A. Tahir da kuma Hadiza Bala Usman. Ana sa ran cibiyar za ta kasance a kan gaba a fagen samar da mafita ta hanyar bincike ga matsalolin tattalin arziki Nijeriya da kuma bunqasa al’amurran zamantakewar al’ummar Nijeriya.

An haifi Dakta Yusuf Bala Usman a garin Musawa ta jihar Katsina. Mahaifinshi shi ne Durbin Katsina a wancan lokacin. Sannan dan uwansa Sarki Usman Nagogo shi ne Sarkin Katsina. Mahaifiyarshi ‘ya ce ga tsohon Sarkin Kano Marigayi Abdullahi Bayero.

Ya halarci Makarantar Firamaren Musawa da ta Kankiya da kuma ta Minna. Sannan ya shiga Kwalejin Gwamnati ta Kaduna a shekarar 1958. Daga nan ne ya tafi karatu a ‘Unibersity Tutorial College’ daga shekarar 1963 zuwa 1964. Daga nan sai ya shiga Jami’ar Lancaster inda ya kammala karatun Digirinsa a bangaren Tarihi da kimiyyar Siyasa daga shekarar 1964 zuwa 1967. Ya dawo Nijeriya ne a shekarar 1967, bayan dawowarsa ne sai ya zama Malami a Kwalejin Barewa dake Zariya inda ya karantar har ya zuwa shekarar 1971.

A shekarar 1970 ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, inda ya samu digirinsa na Uku wato PhD (Doctorate Degree) a shekarar 1974. Sai ya fara karantarwa a Jami’ar ta Ahmadu Bello dake Zariya a matsayin Malami na wucin gadi, daga nan aka kara masa girma zuwa dawwammen Malami.

An haifi Dakta Yusuf Bala Usman a watan Maris na shekarar 1945, sai dai Allah ya karbi rayuwarsa a ranar 24 ga watan Satumban 2005. Shekaru fiye da 13 da suka gabata. Kafin rasuwarsa, Dakta Yusuf Bala Usman ya assasa Cibiyar Dimokradiya da ci gaban bincike da horaswa ta Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya wato CEDDERT.

Dakta Yusuf Bala Usman, yana sahun farko na masana tarihi a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya tun bayan mulkin mallakan Turawa. Ya yi rayuwarsa kacokaf ne wajen yin karatu da karantarwa, sannan ya yi gwagwarmayar tabbatar da adalci da kuma ci gaba da koyon darasin tarihi. Dakta Yusuf Bala Usman yana ganin yadda marubutan Turawa suka tattara tare da rubuta tarihin mutanen Afrika ta hanyoyi amfani da shaidar rubutu, Yare, labaran Baka da kuma binciken tarihi da nufin bunqasa su (archaeological sources), sun cika binciken na su da son rai da ra’ayyuka.

Dakta Yusuf Bala Usman, ya taimaka matuqa gaya a sashen Ilimi da karfafa binciken Ilimi, sannan yana da burin bunqasa wannan fannin a Nijeriya.

A lokacin rayuwarsa, ya rike shugaban Sashen Nazarin Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya daga shekarar 1979 zuwa 1980. Sannan ya zama shugaban tsangayar Fasaha da kimiyyar zamantakewa ta Jami’ar a shekarar 1977. A shekarar 1978 zuwa 1980 ya zama memba a Majalisar Dattawar Jami’ar. Ya kuma taba zama wakili cikin shuwagabanni masu ba da shawara ga Jami’ar daga shekarar 1976 zuwa 1980.

Daga cikin ayyukan da ya yi lokacin rayuwarsa shi ne ya duba dimbin rubutattun binciken dalibai a matakan Digiri na Biyu da na Uku sama da guda 30.

A lokacin mulkin Soja na Murtala Ramat ya zama memba cikin kwamitin gyara tsare-tsaren hulxa da qasashen waje. Ya tava zama cikin kwamitin sake fasalin kundin tsarin mulki a lokacin Marigayi Murtala. Sannan yana cikin tawagar da aka tura a shekarar 1976 Jamhuriyyar qasar Angola domin tattaunawa kan dawo da zaman lafiya a qasar.

Dakta Yusuf Bala Usman ya zama mashawarci na musamman a tawagar Nijeriya a majalisar dinkin duniya a zama na 31 da 41 a shekarun 1976 da 1986. Kuma ya taba rike mukamin Daraktan Bincike na Jam’iyyar PRP a shekarar 1979 zuwa 1980. Sannan yana cikin zababbun yardaddun kungiyar NLC a shekarar 1978-1980. Ya riqe muqamai daban-daban a rayuwarsa. A Jamhuriyyah ta Biyu a Nijeriya, ya tava zama Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna a qarqashin Gwamnatin Balarabe Musa na Jam’iyyar PRP.

Dakta Yusuf Bala Usman ba kawai ya taskace tarihi da kawo sauyi a Nijeriya ba, sauyinsa ya garzaya har ya zuwa ga fadin duniya baki daya ta hanyar Iliminsa da hangen nesan sa. Ayyukan rubuce-rubucensa sun hada: “Domin ‘Yantar da Nijeriya”: Littafi ne da aka tattara daga karantarwa da yake yi a Aji aka buga a shekarar 1979. Samuwar sauyi a Katsina daga 1400 zuwa 1883 (an buga shi a shekarar 1981).

Rashin amincewar Nijeriya da IMF: tsarin Huldar Kasuwancin cikin gida (an buga a shekarar 1986). Matsalolin Tattalin Arzikin Nijeriya: Matsala da Hanyoyin Magance su (an buga a shekarar 1985). Rashin alkiblar Nijeriya (an buga a shekarar 2005). Nazarin Tarihin Daular Sakkwato (an buga a shekarar 1979). Tarihin gwagwarmayar NEPU da PRP (an buga a shekarar 1981).

Wasu ayyukan na shi sun hada da: Ma’aikatan Nijeriya da Matsalar da tattalin arziki ya fada (an buga a shekarar 1982). Rashin ci gaban siyasar Nijeriya; wanda aka buga a shekarar 1982 daga wadansu rubuttuka da aka tattara. Ya jagoranci rubuta da taskace su wanda suka hada da: “Biranen Sabannah” wanda aka buga a shekarar 1979. Nazarin Tarihin Mutanen Borno kafin zuwa Turawan Mulkin Mallaka (an buga shi a shekarar 1983). Ci gaban Tattalin arziki da zamantakewa a Nijeriya (an buga a shekarar 1986). Mu shiga cikin tarihin Nijeriya (shi kuma an buga shi 1985).

Duk waxannan ayyukan na shi da littattafan ya rubuta su ne cikin harshen Ingilishi. Kuma waxannan kaxan ke nan daga cikin ayyukansa na rubuce-rubuce.

Kafin rasuwarsa yana da ‘ya’ya kamar haka; Halima, Attahiru, Zainab, Mariya, Hadiza (Daraktan Hukumar Tashoshin Ruwan Nijeriya wato NPA), Hassan sai kuma Hussain.

A lokacin ta’aziyyarsa, Marigayi tsohon shugaban qasar Nijeriya, Umaru Musa Yar’aduwa da yake tunawa da Dakta Yusuf Bala Usman ya bayyana cewa; “(Marigayin) ya yi faxa da rashin gaskiya da kuma rashin adalci, wannan kuwa rashin adalcin a wata qasa ce ake aikatawa, ko a wani wuri daban, raunanna ce ko zaluntar xaixaikun mutane, ko kuma wasu su zalunci wasu daban. Ya gudanar da rayuwarsa ne wajen fada da al’ummar da suke kokarin samun karfi domin tauye hakkin wasu, da zaluntar mutane a kowanne fanni da mataki na al’umma, wanda ya bayyana su a matsayin raunanan mutane. Ko a gida ne, ko a wurin aiki ne, ko a wurin tattaunawa ne, ko wurin Jawabi ne, yana amfani da iliminsa da tunaninsa da imaninsa wajen yakar rashin adalci. A kowanne lokaci akwai mutane kamarsa, irin waxannan ne suke qoqarin canza al’umma da duniya baki xaya.”

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply