An Nemi Gwamnatin Jihar Kaduna Da Ta Tallafa Wa Manoman Albasa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Mansur Aliyu Samaru

Shugaban kungiyar manoma Albasa da sarrafata tare da sayar da ita, wato Alhaji Sani Ismail Kargi,ya bukaci gwamnatin Jihar Kaduna, da ta tallafawa manoman Albasa da kayan aiki kamar yadda take tallafawa sauran manoma.

Shugaban yayi wannan kiranne yayin da suke zantawa da wakilinmu bisa irin ci gaban da kungiyar ta samu a jihar Kaduna da ma kasa baki daya.

Alhaji Sani Ismaila Kargi, ya bayyana irin nasarorin da suka samu wajen wayar da kan manoma Albasa tare hada kawukansu

waje guda don tallafawa juna tare da kwato ma duk wanda aka zalunta hakkinsa a kungiyance.

Ya kara da cewa a halin yanzu an samu ci gaban kawo Kanfanonin da suke sarrafa Albasa ta hanyoyi daban daban har ma da busar da ita ba tare da an sami rubewa ba a jihar Sokkwato.

Shugaban na jihar Kaduna, ya kara da jinjina ma shugaban kungiyar ta kasa wato Alhaji Aliyu Isa Binji, bisa irin jajircewarsa har ya zamanto Nigeria ce kasa ta biyu a Afrika wajen noman Albasa,  sannan kuma itace kasa ta bakwai a duniya.

Daga karshe, Alhaji Sani Ismaila Kargi, ya yi kira ga manoman Albasa tare da sauran al’umma masu shaawar noman Albasa dasu zo domin a tafi tare don a yi masu rajistan zama ‘yan kungiyar na dindindin.

Share.

About Author

Leave A Reply