Arewa Ina Mafita?

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Duba da yadda abubuwa ke faruwa a kasar mu ta Nijeriya, dukkan mai hankali yasan arewacin Nigeria ya shiga halin ni’yasu saboda tarin matsaloli da suka yi wa yankin katutu.

Arewa ita ce bangaren da ta fi kowacce bangare zaman lafiya a baya, zamani ya shude wanda ta kai ga matafiya masu safara a cikin yankin basu da wata fargaba ta tsaro ko tashin hankali. Ga masu zuwa kudu kuwa, a duk lokacin da mutum ya tsallako yankin arewa to shi kenan hankalin sa zai kwanta domin bashi da fargaba ta yanfashi, rashin tsaro ko kuma tashin hankali.
To a yanzu abun ya sauya zane, arewacin Nijeriya ta zama yanki mafi hadari ga rayuwa da kuma dukiyoyin mutane sakamakon ayyukan barayin daji, masu garkuwa da jama”a, rikicin boko-haram inda masu ina da kisa suke yadda suka ga dama suke cin karen su babu babbaka, ganin yadda rayukan Yan Arewa suka zama tamkar na kiyashi dukiyoyin su kuwa su da kansu suke dauka su kaiwa barayin daji masu garkuwa da jama’a domin ceto rayukan su saboda gwamnati ta gaza wajen kare lafiya, mutunci, dukiya da rayukan su.
Wannan hali ya sanya harkar noma, kasuwa da sana’oin hannu da sune abubuwan dogaron Yan Arewa sun sami nakasu da babban koma baya a inda suka kara kuncin rayuwa, talauci da zaman kashe wando sakamakon rashin aiki da durkushewar tattalin arziki.
Sannu a hankali kuma sai ga shi nuna tsangwama da kiyayyar Yan Arewa ta zama ruwan dare a wajen Yan Kudu inda a yanzu Yan Arewa rayuwar su da dukiyoyin suka zama ba’a bakin kome ba. Da wani abu ya faru sai muga an fake dashi ana kashe Yan Arewa, a wawashe tare da kone masu dukiya. A kwanannan munga yadda aka fake da zangazangar ENDASAR wajen kaiwa Yan Arewa farmaki a wasu Jihohin Kudu amma abun shiru babu wani matakin da aka dauka banda kokarin Tsohon Gwamnan Sokoto Mai-Girma Alhaji Attahiru Bafarawa yayi wajen hada kudin bayanai na irin illar da akayiwa Yan-Arewa . Amma kawo yanzu babu wani mataki da aka dauka domin gurfanar da wayanda sukayi wannan aika aika kawo yanzu.
A baya mun yi bayani lokacin da Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya debawa Fulani Makiyaya wa’adin kwana bakwai su bar Jiharsa, cewar wannan ba ra’ayin sa bane shi kadai ra’ayin dukkan al’ummar sune baki daya na fara aiwatar da shirinsu na korar ‘yan Arewa. Ba a dade ba Sunday Ighoho ya jagoranci kai hari gidan Sarkin Fulanin Oyo inda aka kone gidan da kashe wasu daga cikin ‘yan gidan. Amma shi Sunday a yanzu maimakon gurfanar da shi a gaban shari’a sai aka mayar da shi gwarzan fara kawar da ‘yan arewa daga yankin kudu maso yamma na manufofin dake boye a wa’adin da Gwamnan Ondo ya bai wa Makiyaya su bar yankin. Wanda aka yi amfani da shi a matsayinsa na babban lauya masanin doka da kuma tsohon shugaban Kungiyar Lauyoyin Nigeria ta kasa a matsayin zakaran gwajin dafi na auna yadda za”a kori Yan-Arewa.
Idan har lauya mai matsayi na Gwamnan Ondo zai fito ya bada nasarwar da ta take doka to mai ya rage wajen Yan Tasha masu neman tada zaune tsaye?
Sai ga shi ana kukan targade karaya ta samu, akan karamin rikici a Ibadan an kai wa Hausawa farmaki inda aka kashe su, aka raunana su, aka kone masu dukiyoyin su. Wannan sun fara nunawa a fili mummunan tanadin da akayi domin fatattakar Yan-Arewa daga kudu. Sannan bugu da kari ya fito da manufar Amotekun wanda ta zama an tanade tane domin muzgunawa Yan-Arewa ganin yadda ta taka rawa wajen kashe Hausawa.
Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki na arewa da su dauki kwakkwaran mataki su gabatar da korafi a gaban Majalissar Dinkin Duniya na irin kisan gillar da akewa Yan-Arewa da wani abu ya tashi a kudu.
A wakar Alhaji Mamman Shata Katsina ya ce: “ana so a taba mu ‘yan Arewa ana tsoron manyan mutane”. Idan muka dubi wannan baitin, shin za mu ce akwai manya a Arewa kuwa?

To a gaskiya ya kamata ‘yan arewa mu farka daga barci kamar yadda Shata ke cewa “mu tashi mu farka Yan-Arewa musan bacci aikin kawai ne”.

Ado Umar Lalu
Shamsu Muhammed Funtua
Lawal Sani Usman
Lawal Saminu

Share.

About Author

Leave A Reply