Ayyukan Alherin Sanata Kabir Barkiya A Kan Sikeli

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Zahraddeen Sirajo

Sanata Injiniya Kabir Abdullahi Barkiya, dake wakiltan Katsina ta tsakiya (Katsina Central Zone) ya yi ayyukan da babu wani sanata da ya taba yin su cikin kankanin lokaci, Babban abin burgewa da ayyukan kaitsaye sun shafi al’umma ne, kuma kan muhimman abubuwan da suke bukata akan lokaci. Sanata Kabir Barkiya, yazama na farko kuma tilo tallin tal da ya zama zakaran gwajin dafi a bangaren hidintawa al’umma da daukan nauyin su gami da tallafa musu ta fuskoki daban-daban.

Cikin wannan gajeran rubutu da zamu gabatar zamuyi duba kan wasu ayyuka kadan kuma na nan kusa-kusa da sanatan aiki yayi domin inganta rayuwar mutanen da yake wakilta.

Kafin nayi nisa zan fara bayyana wani muhimman abun da mutane dayawa basu sani ba game da ayyukan alheri na Sanata Barkiya, aikin daya shafi dukkan al’ummar jihar Katsina bana na yankin da yake jagoranta ba ma kawai. Sanata Barkiya shi ne jigon daya tsayu kai da fata wajan tabbatar da tsarin taffalin nan na NDE da gwamnati taryya ta fito domin rage radadin illar da cutar Corona tayiwa al’umma cewa wannan tsarin ya shafi kowa da kowa. Sune suka dinga zamammaki da kiraye-kiraye gamida jan hankali ga ministan da aikin ke hannun sa tare da bada shawarin ga hanyoyin da za’abi domin tsarin ya ratsa ko’in ya samu kowa da kowa. Badan tsayuwar su ba gaskiyar magana da wasu takaitattun mutane ne kawai zasu amfana da tsarin baze kai ga sako da lungu na ba.

Na takaita muku Sanata Barkiya yana cikin mutanen da suka fara kira da gabatar da takarda a Majalisa domin fara wannan tsarin na bada tallafin. Wannan shi ne wakilci na gari bayan sun gabatar da korafi da takardun neman fara wannan tsarin kuma suka tsayu ganin an karba har sai da aka fara kuma suka tabbatar anyi aikin ta hanyar da ya dace. Bari mu koma zuwa ga wasu ayyukan da suka faru kwanan nan wanda me girma Sanata ya kaddamar wasu yaje da kan shi wasu ya aika wakilan amana suka gabatar a sassa daban daban na yankin da yake wakilta, mafiyawan abubuwan da ayyukan sune na farko a tarihin yankin Katsina ta tsakiya. Wannan da na gabatar shi ne na farko yanzu zan shiga jero sauran a hankali zuwa inda kafina ya kare, kuma duka wadanda zan lissafo ayyuka ne da yayi su karshe karshen shekarar 2020 da ta kare.

2. Sanata Barkiya, ya raba sama buhun takin zamani guda dubu uju (3000) ga manoman rani da damina wanda suka fito daga kananan hukumomi 11 dake Katsina ta tsakiya. Wannan rabo da yayi dubban manoma ne suka amfana da shi, wanda sanadin haka manoma sunyi matukar farin ciki da walwala amfani yayi kyau sun amfana.

3. Sanata Barkiya, ya tona burtsatsen ruwa da bansan adadin su ba aduk yankuna Katsina ta tsakiya cikin birni da kauye, ko’ina ka zaga ruwan sha me tsafta ya wadata ana samu cikin sauki domin amfani, sannan kuma an samar da hanya mafi sauki na gyara burtsatsen koda ya lalace, kuma har yanzu ana cigaba da samar da wasu, domin tabbatar da cewa ruwan sha beyiwa kowa wahalar samu ba.

4. A lokaci guda me girma Sanata Barkiya, ya gina manyan hanyar ruwa a tsarin nan na ‘Zonal Intervention Projects’ a kananun hukumomin Kurfi, Batsari, Dutsinma dukan su domin inganta rayuwar yankin da kula da tsaftar muhallin su.

5. Manyan Daman Samun Ayyukan Yi (Leburanci) wannan wani babban shashi ne na ayukan da yayi musamman ga mata da matasa marassa aiki masu karatu me zurfi da marassa, domin hana zaman banza da kuma tallafawa inganta rayuwar su da suka hada da; sama da mutane 10 sun samu daman tafiya aikin soja, daruruwan wasu sun samu aikin Jinya, tsarin tallafin nan na GT na NDE, FIRS, DSS da kuma sauran su.

6. Gyara gami da inganta kusan dukkan makarantun Primary da Secondary, wasu daga cikin su sun hada da; Birchi Model Primary School, Command School Barkiya, da kuma Batlada Community School da sauran su. Anyi wannan ne domin a gyara tsarin makarantu yara su samu ilimi me amfani cikin nutsuwa.

6. Tsarin Koyar Da Sana’o’in Hannu Ga Matasa Domin Dogaro Da Kai: A karkashin wannan tsarin me suna ‘Barkiya Youth Skills Acquisition Program’ an koyar da matasa sama 100 yanda zasu koyi ilimi dasa Sola da kuma gyarata sannan ana basu ‘dan kudin kashewa a yain da suke koyan kuma aka hada musu da kayan aikin bayan an yayesu.

7. Tsarin Karfafa Mata da Tallafa musu me suna; ‘Barkiya Women Empowerment Program’ a karkashin wannan tsarin mata sama da 1200 aka basu jarin kudin Naira dubu 10 domin su fadada harkokin kasuwancin su.

*Ayyukan Sa Domin Inganta Harkokin Tsaro*

Wannan harkar ta tsaro, lafiya da dukiyoyin al’umma babban bangare ne kuma me muhimmancin gaske wanda Sanata ya taka rawar da za’a gani sosai wajan ganin an magamce rashin tsaro da fama da hare-haren ‘yan bindiga a yankin da yake wakilta a Katsina. Duk wanda yake bibiyan irin kudurorin da Sanata Barkiya yake gabatarwa a zauren Majalisa kullum sai ya kawo magana kan matsalar tsaron nan, shawarwari da neman hanyoyin magance su. Ya bada tallafin ka canyan aiki ga jami’an tsaro da suka hada ‘yan sanda, ‘yan banga da sauran su domin tabbatar da ana aiki cikin kwarewa da tafiya da zaman.

Daga Zahraddeen Sirajo Abbas
zahradeensirajoabbas@gmail.com

Share.

About Author

Leave A Reply