Azumi: Jam’iyyar APC Ta Raba Tallafin Sama Da Naira Biliyan Daya A Zamfara

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara, karkashin jagorancin Tsohon Gwamna, Abudul’aziz Yari Abubukar ta kaddamar da rabon tallafin abincin Azumi ga al’ummar na sama da Naira Biliyan daya.

Shugaban kaddamar da shirin tallafin abincin Azumin, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana cewa, jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara, Hon. Abdul’aziz Yari shi ne ya wakilta da wasu jigon Jam’iyyar ta Kasa.

Sanata Marafa ya kara da cewa, wannan tallafin na abincin azumi da Jigon Jam’iyyar ya saba rabawa a duk shekara, a jiya Lahadi sun raba tirelar abinci 130, wanda kudinsu ya kama naira Biliyan daya da dubu dari uku da ashirin da takwas.

A nan take, Sanata Marafa ya bayyana yadda kason abincin zai kasance kamar haka: Kowace Karamar Hukuma za ta samu tilera biyar, wadanda suka hada da Shinkafa, Wake, Masara da Gero. Amma  Karamar Hukumar Gusau a matsayinta na hedikwatar Jihar za su raba tirela 10. Sauran kayan abinci da tirela Hamsin za a raba ma Marayu da gajiyayyu da musakai da kungiyoyi.

Sanata Marafa ya kuma tabbatar da cewa, kada kowa ya bada kudin wanda aka ba shi tallafin abinci. Domin kuwa Hon. A.A Yari ya biya kudin motar kai wa ga kowacce Karamar Hukuma. “Don haka duk wanda ya ce, ku ba shi kudi ku kawo mana kararsa” inji Sanata Mafara.

Wanda ya wakilci uwar jam’iyyar APC ta Kasa, Sanata Abba Aji ya jinjinawa jigon jam’iyyar APC, Hon. Abdudulaziz Yari kan wannan namijin kokari da ya yi na tallafawa al’ummar Jihar Zamfara.

Sanata Abba Aji ya kuma tabbatar da cewa, har yanzu Jihar Zamfara ta Jam’iyyar APC ce. “Ku shaida ne al’ummar Jihar Zamfara, kuma a yau kun sake tabbatar mana da haka.” Inji shi

 

Share.

About Author

Leave A Reply