Azumin Ramadan: Wata Kungiya Ta Gargadi ‘Yan Kasuwa Kan Kara Kudin Kayan Masarufi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Peace Revival and Reconciliation Foundation of Nigeria’  ta gargadi ‘yan kasuwa a Nijeriya dasu guji kara kudaden kayan masarufi a daidai lokacin da ake shiga watan Ramadan mai alfarma.

Shugaban kungiyar, Fasto Yohanna Buru, ya bayyana haka a tataunawarsa da manema labarai a garinKaduna ranar Lahadi.

Fasto Buru ya kara da cewa, kungiyar na shirin hada kan ‘yan kasuwa musulmai da kiristoci na arewacin kasar nan don fadakar dasu kan illar kara kudaden kayan masarufi a wannan lokacin na watan Ramadan.

Ya ce, babbar manufar haka shi ne, yadda musulmi za su samu saukin gudanar da ibadan azumi ba tare da wani wahala ba, ya ce, wanna fadakarwar sun fara ne tun daga shekarar 2015.

“Mun kuma tattauna mahimmancin watan Ramadan tare da fadakar da ‘yan kasuwa akan illar da ke tattare da kara kudaden kayan masarufi haka siddan da kuma boye kayan abinci don su yi tsada,” inji shi.

Ya kuma kara da cewa, zuwa yanzu an samu Musulmai da Kiristoci fiye da 100 da suka amince su shiga kasuwanni don tatauna da ‘yan kasuwa akan illar kara kudaden abinci a wannan lokacin.

Ya kuma nemi al’umma Musulmi su taikama wa nakasasu da marasa karfi da marasa aiki da tallafin a wannan watan na Ramadan.

 

Share.

About Author

Leave A Reply