Babban Sufeto, Zanga-zangar #EndSARS Da Bayyanar Sabon Tsarin ‘Yan Sanda, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A tarihin Nijeriya, wasu tsirarun baragurbi a rundunar ‘yan sandan sun yi ta yin ayyukan assha da ya shafa wa gaba daya rundunar kashin kaji. Wanda hakan ya sa mutane suka samu wani irin bahagon ra’ayi dangane da rundunar ta ‘yan sanda a Nijeriya. Abin ya kazanta ne yayin da aka yi ta samun matsalolin yawaitar kisa ba tare da ka’ida ba, rashawa, amsar cin hanci, da kwace daga bangaren su wadannan baragurbin ‘yan sandan.

A lokacin da ya zama babban sufeton ‘yan Sandan Nijeriya a shekarar 2019, IGP Muhammad Adamu ya zo da wasu tsare-tsare na kawo gyara da yin garanbawul ga matsalolin da ke addabar wannan runduna. Ya yi ta bin hanyoyin yin gyara don dakile afkuwar irin zanga-zangar da ake ta faman yi yanzu a sassan kasar nan.

Daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci daga shugaba mai nagarta shi ne ya iya kudurtar aniyar kawo gyara ba tare da wani taraddadi ba. A ranar Lahadin da ta gabata ne Babban Sufeton ‘yan sanda, Adamu Muhammad ya sanar da rushe rundunar musamman mai kula da harkar fashi da makami, wanda wannan ya nuna irin hangen nesan da babban sufeton yake da shi. Wannan kuma ya nuna cewa Babban Sufeton ‘yan sandan ya shirya yin gyara a gabadaya rundunar ta yadda za ta daidaita da sauran takwarorinta na duniya. Rushe Rundunar SARS na daya daga cikin matakan da za a dauka wurin kawo gyara.

Duk wannan ba abin mamaki ba ne bisa la’akari da irin aiki tukuru da Babban Sufeton ‘yan sandan ya yi a shekaru 10 da ya kwashe yana aiki da rundunar ‘yan sanda ta kasa da kasa ‘Interpol’.

Babban aikin da ya rataya a kan kowacce gwamnati shi ne kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma. Domin cimma wannan buri kuwa, dole ne ya zama tsarin gudanarwa na rundunar ‘yan sanda ya zama ta yi daidai da muradin kyautatawa al’umma. A kasashe da dama, musamman wadanda suke kan tsarin gwamnati irin na Nijeriya, akwai bangarorin jami’o’in tsaro mabambanta, wadanda suka hada da ‘yan sanda, dukkaninsu aikinsu shi ne tabbatar da doka da oda.

Kokarin Babban Sufeton ‘yan sanda, Adamu na ganin ya sauya fasalin rundunar ya na ci gaba da samun tagomashi ne saboda irin gudummawar da ya jima yana samu daga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda a ranar Litinin a Abuja ya sanar da rushe rundunar SARS a matsayin mataki na farko na sauya fasalin rundunar ‘yan sandan Nijeriya. Haka kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin cewa duk wani abu na rashin da’a, karya doka da rundunar ta SARS ta taba yi a kawo shi domin bin kadi.

Nijeriya kasa ce da ke tafiya bisa turbar Dimokradiyya, kuma dole ne dabi’a da gudanarwar shugabannin da aka zaba a wannan tsari ya zama daidai da tsarin. Daya daga cikin abubuwa masu ban sha’awa da Dimokradiyya shi ne yadda mutane za su bayyana ra’ayinsu, su kuma fadi abin da suke so a yi musu, wasu lokutan ma har su yi zanga-zanga. Gwamnatin Buhari ta sake tabbatar da kimar Dimokradiyya a  Nijeriya ta hanyar sauraron koken masu zanga-zanga inda nan da nan ya bada umurni aka rushe rundunar FSARS.

Su shugabanni na nagari a kodayaushe a shirye suke su dauki nauyin kowanne irin aiki na kasa da su suka aikata. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kwatanta haka, yayin da ya jajanta tare da bada hakuri ga iyalan wani da aka kasha yayin zanga-zangar kin jinin rundunar SARS a Jihar Oyo.

Akwai bukatar mu yi adalci wurin bayyana irin kokarin da wasu daga cikin ‘yan sanda ke yin aikinsu bisa ka’ida da nuna kwarewa. Ko shugaba Buhari ya san da haka, domin har ya fadi cewa akwai mutane da yawa maza da mata daga rundunar ‘yan sanda wadanda ke aiki bisa ka’ida da kiyaye dokoki.

Saboda irin tsarin gudanarwa da Babban Sufeto, Adamu ke da shi, da kuma kyakkyawar alakar da yake da ita ga sauran kwamishinonin ‘yan sandan jihohi, wannan sai ya samar da kusancin aiki mai kyau a tsakaninsu. Sannan mu yi la’akari da kokarin babban sufeton na tsarkake Babban Birnin Tarayya daga barna da dangoginta, wannan ne ma ya sa ya nada BAla Ciroma a matsayin Kwamishinan ‘yan sanda na Abuja din.

Idan mu ka kalli Babban Sufeton ‘yan sanda, Adamu za mu ga cewa kwararren masanin harkar tsaro ne, wanda ke da kwarewar aiki ta zamani. Ya yi aiki da rundunar ‘yan sanda ta kasa da kasa a Jihar Legas daga shekarar 1989 zuwa 1997. Shi ne dan Nijeriya na farko da ya fara zama mataimakin Shugaba a Sakatariyar Rundunar ‘yan sanda ta kasa da kasa da ke Lyon  shekarar 1997, inda ya yi aiki a sashen tattalin arziki da barnar da ta shafi kudi daga shekarar 1997 din zuwa 2002. A shekarar 2002 ne ya zama dan Afirka na farko da ya fara rike mataimakin Darakta da ke kula da yankin Afirka a rundunar ‘yan sandan ta kasa da kasa, har zuwa shekarar 2005. Haka nan kuma shi ne dan Afirka na farko da ya fra zama Darakta a rundunar ‘yan sanda ta kasa da kasa ‘Interpol’ daga shekarar 2005 zuwa 2007.

Bayan da ya dawo Nijeriya ne aka nada shi a matsayin Daraktan da ke kula da wanzar da zaman lafiya da horaswa a hedikwatar rundunar ‘yan sanda da ke Abuja. Daga shekarar 2013 zuwa 2015 ne kuma aka yi masa mukamin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, sannan kuma ya zama kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Enugu.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).

Share.

About Author

Leave A Reply