Babbar Sallah: Shugaban Majalisar Nasarawa Ya Nemi Musulmi Su Yi Wa Kasa Addu’a

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban majalisar dokokin jihar nasarawa, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bukaci al’umma Musulmi su yi amfani da wannan lokaci na bukuwan babbar salla wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya da cigaban tattalin arziki.

Shugaban majalisar ya yi wannan bayani ne a takardar sanarwa da jami’in watsa labaransa, Mr Jibrin Gwamna, ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a garin Lafia ranar Talata, ya kuma ce dole mumunai su cigaba da yi wa kasa addu’a tabbatar da zaman lafiya da cigaba.

Ya kuma bukaci Musulmi su yi amfani da wannan lokaci wajen neman Allah ya kawo wa kasar nan dauki wajen maganin matsalar tsaro da ake fuskanta a sassan kasar nan.

Ya kuma nemi Musulmi su kara karfafa dankon zumunci da ‘yan uwantaka a tsakanin su da kuma taimaka wa marasa karfi a cikin al’umma.

Shugaban majalisar ya kuma nemi Musulmi su tabbatar da bin doka da oda a duk inda suka samu kansu da kuma yi wa shugabanin addu’a a dukkan lokaci.

 

Share.

About Author

Leave A Reply