Babbar Sallah: Yan Sandan Jihar Neja Sun Ce, Ba Su Samu Rahoton Aikata Wani Laifi Ba

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta ce, ba ta samu wani rahoton aikata laifi ba yayin bikin Eid-el-Kabir a jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda Adamu Usman ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) a ranar Alhamis a Minna.

Ya ce, rahotanni daga qananan hukumomi 25 sun nuna cewa an gudanar da bikin cikin lumana ba tare da samun barazana ga rayuka da dukiyoyi ba.

“Mun yi bukukuwan Sallah ba tare da vata lokaci ba a duk faxin jihar kuma ba a kama kowa a lokacin da kuma bayan bikin ba. An gudanar da dukkanin bikin ba tare da samun barazana ga rayuka da dukiyoyi ba a faxin qananan hukumomin 25,” in ji Usman.

Ya yaba wa mazauna garin bisa haxin kai da suke bai wa jami’an tsaro da ke aiki a jihar.

Usman ya yi kira ga mazauna yankin da su ci gaba da marawa qoqarin rundunar baya ta hanyar samar da bayanai masu amfani kuma cikin lokaci waxanda za su taimaka wajen hana aikata laifuka da kuma cafke masu aikata laifuka.

Ya ce, matakan tsaron da aka riga aka sanya za su ba mazauna ci gaba da harkokin kasuwancin su ba tare da wata matsala ba.

“Abin da kawai muke buqata daga jama’a shi ne bayani a kan lokaci game da motsin wasu mutane, don xaukar matakan tsaro,” in ji Usman.

Share.

About Author

Leave A Reply