Bayajiddan Kinkinau Ka Gaza!

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Zorro Jnr.

Kwanakin baya masana suka fitar da rahotan dake nuni da Nijeriya na cikin jerin kasashe mafiya hadari da al’umma ke rayuwa cikinsu wanda hakan ke nuni karara kan Gazawar jagarori kan sha’anin tsaro da kuma fanin harkar da lafiya kai har ma da tabarbarewar tattatalin arziki da muke fama da shi a wannan kasa ta mu. Zahirin gaskiya babu wani mawalati ko walwala ga dukkan al’umma da suka rasa daya daga cikin ukun nan; Tsaro, lafiya, tattalin arziki.

Kwanakin baya wanda basu gaza 60 ba an yi wa Sarkin Musulmi caaa daga bangaren masu kare  gwamnati, biyo bayan wani dan ‘tabin alli’ da ya yi a kan halin ni-‘ya su da Arewacin Nijeriya ke ciki kan sha’anin tsaro. Sultan ya bayyana cewa arewacin Nijeriya ne wuri mafi hadarin zama a yanzu. Muddin mutum ba shirgin guna ba ne yana da lafiyar kwakwalwa, ba kuma Karen Farauta ba ne, ya san maganar da Sarkin Musulmi ya yi, gaskiya ce gayan ta.

Babu bambanci tsakanin Arewacin Nijeriya na yanzu da wurare irinsu Somaliya da Afganistan sakamakon hare-hare na ta’addanci da suka yi yawa a cikinta. Arewa maso gabas tuni sha’anin ta’addanci da keta na Boko Haram sun murkushe ta, cikin makonni da basu gaza uku ba an kai wa manoma Bayin Allah masu fafutukar kai wa bakin salati hari wanda aka kashe akalla mutum 60. A rahotan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta bayyana adadin wanda suka rasa rayukansu sun kai mutum 104. Sai dai wani abin ban takaici mara kuma dadi, shugaban Nijeriya ta hannun mataimakinsa na musamman, wato Garba Shehu ya ce basu samu sahalewar jami’an tsaro ba suka fita aikin gonar. To abin tambayar shi ne dama a Nijeriya sai an nemi izini ake zuwa gona? Yaushe lalacewa da tabarbarewarmu ta kai haka? Me ya sa ba a sanar damu ba kamar yadda ake fitar da sanarwar karin kudin wuta ko na fetur?

Arewa maso yamma ita ce ake mata kallon zaman lafiya da lumana amma a yanzu ita ma ta hadu da nata karfan kafar, tunda an jarrabe ta da ‘yan bindiga masu sace mutane su karbi kudin fansa. Wutar kamar wasa ta kunno kai daga Zamfara sakamakon rashin ingantaccen jagaronci, wacce kuma aka bar ta ana ta sharholiya har sai da ta fada Sokoto ta rarrafa Katsina da hanyar Abuja zuwa Kaduna. Yanzu ta kai makura har Zariya ko na ce har kuryar Babbar Jami’a ta Arewa wato A.B.U Zaria.

Sakamakon gazawa ta shugabanci tun daga sama har zuwa kasa, a cikin garin Zariya suka kutsa suka dauki malamin jami’a mai matakin digri uku (PhD). Suka dawo suka yi zabarin wani shugaban tsangaya guda a Kwalejin Fasaha na Nuhu Bamalli duk a Zariyan. Dukkan wadannan sai da aka biya kudin fansa sannan aka ga keyarsu. Ana kuma cikin wannan hali na dar-dar sai suka canza salo suka fara tsayawa kan hanya su budewa motar dake tafiya wuta su kashe jama’a. Akwai motar da suka budewa wuta suka harbi mutum a mukamiki amma saboda rashin imani a haka suka so su tafi da shi, sai da suka ga abin ya ci tura sannan suka bar shi a wurin cikin mawuyacin hali.

An sace mai rawanin an kuma yi awon gaba da jagoran jam’iyya duk a jihar Neja. Abin ya yi tsamarin da suka dauke mai jan kunne dan asalin Amurika wanda sai da ita Amurkan ta turo dakarunta suka shiga jejin suka kwato dan kasarsu tilo. Ya isheka mamaki a ce akan mutum guda an zo daga wata uwa duniya kuma an kwatoshi, amma sauran bayin Allah da suke ‘yan kasa an barsu su yi yadda za su yi da kansu. Wato irin abin da Bahaushe ke cewa, kowa ya iya Allonsa ya wanke ya sha.

Su dama irinsu Kaduna sun yi kaurin suna da rigimar Kabilanci da na Addinai. A kai, a kai rayuka zuba suke kamar na kiyasai. Babu dama ka ji kunne shiru domin kana bude Rediyo za ka ji ance ‘yan bindiga sun hallaka mutane a Birni Gwari. Sun kai hari Kagoro, sun sheke mutanen kauye kaza da kaza. Dukkan wannan abubuwa na rashin dadi dake faruwa wai a kar kashin mulkin mai gaskiya ne Buharin talaka.

Arewa ta tsakiya musamman irinsu Filato da Binuwai, da ma can sun ji jiki a kan rashin zaman lafiya sai kuma ga shi an samu wannan garmashular gwamnatin wadda bata da wani aiki sai kokarin kare kanta ba wai al’umma da suka zabe ta ba. Abin takaici duk wannnan abin da ke faruwa babu ruwansu domin shi lamba dayan zai bar Garbati ne da sakon “shock” da “strong condemnation” daga wannan lokaci a wuce wurin ba za ka kara jin duriyarsa ba, indai ba taron jam’iyyarsu ta APC ba ne ya taso ko kuma za a yi zaben cike gurbi. To nan za ka ga zarra, a fito dubu 30 -30 na soja da dan sanda domin kare Dimokradiyya ‘yar Kinkinau.

A jiya na gani a labarai cewa shugaban kasa Buhari ya tafi hutu maihaifarsa ta Daura. Kuma zai kai mako daya a garin. Shin kuna ganin akwai wanda idan aka sace mutum 60 ‘yan sakandare a Legas kuma ya yi katarin zuwa Apapa bude titi, shin Oba na Legas da Oni na Ife za su yi masa shiru? Gidajen Rediyo da na Talabijin da jaridun kudu maso yamma ba za su yi yaga-yaga da shi ba? Toh, mu ga shi a kusa da shi a Kankara an kwashe ‘yan makaranta kamar zabbi kowa ya yi shiru abinsa. Ita gwamnatin na kokarin rage adadin yawan mutanen daga 600 zuwan yanda ba za a ga gazawarta ba, ‘yan Soshiyal Midiya sun yi aikin su “manjo ka gaza” shi kenan fa iyakar abin da za a yi.

A kudu ‘yan yahoo aka kashe amma suka hadu karfi da karfe sai da aka ruguje musu Rundunar SARS sannan kuma aka kirkiri wani kwamiti da zai ji korafinsu. Mu ko a Arewa bayajida ya zo Daura kowa burinsa a sa masa rana ya je ya sauke farali a kwanar Mugu. Babu wanda ya isa ya fada masa ya gaza ta ko’ina, kai har a sha’anin kula da da iyali shi ba jagora ba ne. Tunda ba a taba samun zamanin da aka yi harbi da bindiga a Villa ba sai sanadin rikicin basasar da ta faru tsakanin Iyalinsa Aisha da kuma Tunde wato Firamistan Nijeriya na wannan lokaci. Mu ci gaba da yin gum har munafurcinmu ya karasa mu, mu ci gaba da nuna babu matsala har matsalar ta fi karfin magani. Maluman addini a yi ta addu’a a masallatai cewa wannan abu dake faruwa makircin ‘yan kudu ne akan Buhari da Musulunci irin yadda da gobarar “END SARS” ta taso ya garzayo gida shi da mukarrabansa a ke ta fada cewa so ake a ture shi daga mulkinsa don shi dan arewa ne. Dama naku ne? Allah na za ta na Legas ne. To da suka zo me ya sa baku fada musa za ku goya masa baya a rigimarsa da ‘yan Kudun amma shi ma kuna bukatar abu daya tal “TSARO”, idan ya yi haka to ‘Jabbama’.

Share.

About Author

Leave A Reply