Bayan Shekara 5: Matakan Buhari Don Tabbatar Da Dimokradiyya A Nijeriya, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kololuwar ci gaban gwamnatin dimokradiyya a wannan karni na 21 shi ne kokarin hade bangarorin mulki wuri guda. Wannan kuwa shi ne babban matsalar dimokradiyyar Nijeriya tun 1999. Kafin yanzu, mun shaidi yadda gwamnatocin baya ke cin mutuncin kujerar mulki. Batun bayar da damar cin gashin kai ga Kananan hukumomi, majalisun jihohi da kuma bangaren shari’a. Abin da ya bayyana shi ne gwamnatocin baya sun yi ta yin siyasa ne da wadannan lamurran.

Saboda rashin muhimmanta dimokradiyya, shugabanni sun kawar da kawunansu ta yadda gwamnatocin jihohi ke cin karensu ba babbaka. Majalisun jihohi da bangarorin shari’a sun kasance marasa karfi da katabus. Ta yadda ba su iya gudanar da ayyukansu yadda kamata, ta yadda dole sai sun koma ga gwamnan Jiha domin rokon abin da za su gudanar da aikinsu.

Da zuwan gwamnatin Buhari a shekarar 2015, duk da mugun baki da alkaba’I daga makiyan Nijeriya, gwamnatin sai ci gaba da nasarori take samu musamman a bangaren ciyar da dimokradiyya gaba.

Daya daga cikin wadannan nasarorin har da batun take hakkin da gwamnatoci suka dade suna yi wa kananan hukumomi. Saboda damuwa da irin halin da kananan hukumomi suke ciki, wanda sune ke kusa da talakawa, ya sa Shugaban Kasa Buhari a watan Yunin 2019 ya rattaba hannu kan dokar bayar da cin gashin kai ga kananan hukumomi. Ta yadda za a rika tura musu kudinsu kaitsaye daga asusun gwamnatin tarayya.

Ba iya nan ba, Shugaban Kasa Buhari ya fahimci muhimmancin bayar da ‘yanci ga bangaren majalisun jihohi da bangaren shari’a. Sa hannu ga doka ta 10 na shekarar 2020, masana kundin tsarin mulki sun ce ta yi daidai bisa la’akari da ikon da sashe na 5 na kundin tsarin mulkin Nijeriya 1999 ya ba shugaban Kasa.

A lokacin rattaba hannu kan dokar, Shugaban Kasa Buhari ya ce: “Wannan gwmanatin za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wurin ganin ta kiyaye mutunci da kimar dimokradiyya a Nijeriya”.

Dokar an sa mata hannu wanda zai taimakawa bangaren shari’a da majalisun jihohi a fadin jihohi 36 da ake da su a Nijeriya. Wanda hakan zai taimaka wurin ceto su daga muguntar gwamnonin jihohi, ta yadda za su rika samun kudadensu kaitsaye daga asusun gwamnatin tarayya.

Da wannan, alkalai a jihohi za su tsira dga tursasawar gwamna ta yadda zai sa su yanke hukunci bisa son rai.

Sannan kuma sauran bangarorin gudanarwan za su samu ‘yancin cin gashin kansu a jihohi, ba tare da wata tawaya daga ikon da suke da ita ba.

Masu ruwa da tsaki suna ci gaba da yaba wannan sa hannu kan dokar, inda suke cewa lallai za ta taimakawa dukkan bangarorin gwamnati, wanda kuma hakan ke nuna an samu gwamnati mai ba kowa ‘yancinsa. Su ma manyan lauyoyi sun yi yabo matuka kan wannan doka.

Shugaba Buhari dai ya rufe ido ya yi abin da ya dace. Kundin tsarin mulki da ma cewa ya yi kudaden gudanarwa na bangaren majalisa bai kamata ya rika zuwa daga bangaren gudanarwa ba.

Sai dai su gwamnonin jihohi ba su bada hadin kai, domin wai har sun kafa kwamitin da zai yi nazarin abin ya basu shawara. Abin da ya fi dacewa ga wadannan gwamnoni shi ne su hada karfi da karfe wurin taimakawa Shugaba Buhari a wannan babban aiki na bunkasa Dimokradiyyya.

Buhari ya yi abin da ya dace ta hanyar rattabawa wannan doka hannu. Wannan na daga cikin matakan farko na tsamo dimokradiyya, domin sanin kowa ne, gwmanonin jihohi suna da karfin da ya wuce ka’ida.

Wasu jihohin suna tafiya ne kan tsarin mulkin jam’iyya daya. Wanda ya sa wasu gwamnonin ke gudanar da jihohinsu ta hanyar mulkin kama karya. Hakan kuma ya sabawa tsarin dimokradiyya. Wannan ‘yanci da aka ba majalisun jihohi da bangaren shari’a zai basu damar yin adalci a ayyukansu.

Kawai abin da za a yi shi ne a rika bibiyar yadda suke gudanar da wannan dama da a ka basu, ta yadda zai zam sun yi abin da ya dace. Zai zama Kungiyoyin fararen hula za su taimaka wurin sa ido da bibiyar wadannan bangarori biyu na gwamnati.

Sannan a irin wannan yanayi na bibiyar bangaren shari’a da majalisun jihohi, kafafen watsa labarai da ‘yan jarida suna da rawar da za su tka. A takaice dai, dole ne dukanmu mu tashi tsaye wurin ganin wannan buri na Buhari na cin gashin kan bangaren shari’a da majalisun jihohi ya kai ga nasara.

Abin da Buhari ya yi shi ne bin umurnin kotu, domin tun a shekarar 2013 wata babbar kotun tarayya ta yanke hukuncin a sakarwa majalisun jihohi da bangaren shari’a mara, a wata shari’a wacce kungiyar JUSUN ta shigar da kara.

A hankalce, ba zai yiwu a ce muna kan tsarin dimokradiyyar da tubalinsa shi ne rarrabuwar iko ba, amma kuma a ce gwamnonin jihohi ne ke juya shugabannin sashen shari’a na jiharsu, ta yadda sai sun roke su kudaden gudanarwa.

A tsoron da wasu marasa hangen nesa ke yi na cewa, toh me zai faru idan Shugaban Kasa ya janye ko ya dakatar da zartas da wannn oda. Ai ba zai yiwu mutum mai dattako irin Shugaba Buhari ya aikata irin wannan ba. Wasu ma sun ce a mayar da lamarin kotu ne. Toh ribar me za a ci idan aka ci gaba da jayayya kan wannan al’amari dai zai kawo ci gaba?

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC)

 

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply