Bikin Sallah: Kungiyar NASFAT Ta Nemi A Yi Wa Buhari Addu’a

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban kungiyar NASFAT, Imam Abdul-Azeez Onike, ya bukaci al’umma musulmi su kara kaimi wajen yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, addu’ar samun nasara a kan matsalar tsaro da ake fuskanta a halin yanzu a fadin tarayyar kasar nan.

Imam Onike, ya bayyana haka ne a sakon da ya aikata wa al’umma na bikin sallah, ya ce, hakan ya zama dole musamman in aka lura da dinbin matsalolin tsaron da ke fuskanta a halin yanzu’’.

Ya ce, ya kamata a yi wa shugabanin a dukkan matakai addu’ar samun nasara akan matsalolin da ake fuskanta, ya kuma yi addu’ar Allah ya kawo mana karshe wannan matsalar da ake fusanta ya kuma bukaci shugabanin su yi adalci a harkokin su na shugabanci tare da jin tsoron Allah.

 

Share.

About Author

Leave A Reply