Budurwar Da Ta Wulakanta Satifiket Din NYSC Ta Nemi Afuwa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Budurwa mai suna RABI’AH Bashir Lawal, wacce a makon da ya gabata hotunanta wanda ta wulakanta satifiket din NYSC suka karade kafafen sada zumunta ta nemi afuwan hukumar.

Ita dai Rabi’a ta yi hoto ne yayin da ta wulakanta satifiket din shaidar kammala hidimar kasa. Ta dukunkuna shi kamar takardar kumshe tsire.

Wannan abu da Rabi’a ta yi ya janyo tofin Allah wadai da cece-kuce musamman a Facebook da sauran kafafen sada zumunta.

Sai dai a wata takardar neman afuwa wacce ta aikewa Hukumar NYSC, kuma Jaridar Tantabara Hausa ta samu kwafi, budurwar ta yi nadama tare da neman afuwa.

Share.

About Author

Leave A Reply