Buhari, Nagartaccen Tsarin Gudanarwa Da Masu Kira Ga Daidaita Fasalin Kasa, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +
Wannan kiraye-kiraye da ake ta faman yi na a daidaita fasalin Nijeriya abu ne mai fuskoki da yawa. Wadanda suka cika kafafen sadarwa da wannan kira sun boye ne a bayan wani abu na daban, da yawansu ‘yan siyasa ne da ke da muradin isa ga madafun iko a shekarar 2023. Daga yadda suka matsa da wannan yekuwa za ka fahimci cewa akwai lauje cikin nadi. Dole suna da wata boyayyiyar manufa.
Wannan shi ne abin da suke aikatawa da sunan daidaita fasalin kasa, saboda hakan ya zamo wani abin izgili da wasa a wurin wasu ‘yan siyasa, wadanda komi za su iya aikata wa matukar burinsu ba zai cika ba. Da irin wannan ne kuma suke yaudarar mutanen da basu san gaskiyar hakikarsu ba. Haka nan kuma suna samun hadin kai daga wasu ‘yan jaridar da ke da ra’ayi irin nasu.
A kwanakin baya ne Nijeriya ta yi bukin cika shekara 60 da samun ‘yancin kai, wanda hakan na nufin kasar na samun ci gaba ne ba ci baya ba. Wannan yekuwar da ake ta yi a ‘yan kwanakin nan ba komi ba ne cikinta face son rai, mugunta da kyashi.
Ba don Allah suke yin yekuwar a daidaita fasalin ba, tambayar farko da ‘yan Nijeriya ya kamata su rika yi musu ita ce, me aka fi bukata, daidaita fasali ko nagartaccen tsarin gudanar da gwamnati? Abin da Nijeriya ke bukata a yanzu ba daidaita fasalin kasa ba ne, ana bukatar tsarin gudanarwa mai inganci, nagarta, da gaskiya ne.
Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tun shekarar 2015 ta dauki duk wani mataki da ya dace wurin ganin ta samar da nagartacciyar gwamnati wacce za ta tafi da kowa ba tare da nuna bambanci ba. Alhali yanzu su masu yin wannan yekuwar ba za su iya yi wa ‘yan Nijeriya bayanin me suke nufi da daidaita fasalin kasa ba da suke ta faman zuba turanci a kai a kafafen sadarwa.
Wannan wani shiri ne na rikita lamurra kafin zuwan zaben shekarar 2023. Irin wadannan mutane da ma ba su kaunar zaman lafiya, burinsu shi ne a yi ta hayaniya da hargitsi ba gaira ba dalili.
A takaicen takaitawa, tsarin yadda Nijeriya ta gangaro har zuwa zama jamhuriya abin a yaba ne. Dalilin samar da jihohi a shekarar 1967 wani abu ne da ya afku domin tabbatar da hadin kan kasa, wanda Shugaban Kasa a lokacin Janar Yakubu Gowon ya yi.
A cika Nijeriya shekara 60 da samun ‘yanci, fiye da kowanne irin lokaci a tarihi yanzu kasar nan ta fi bukatar hadin kai fiye da komi. Hannu daya ba ya daukar jinka. Su masu wannan yekuwar burinsu shi ne a koma wa tsarin da kowanne yanki zai rika yin abin da ya ga dama. Irin wannan tunanin ne ya haifar da yakin basasan da aka tafka na Biyafara. Wanda har zuwa yau din nan Nijeriya ba ta gama farfadowa daga illarsa ba.
Zancen gaskiya shi ne, idan ana maganar daidaita fasalin kasa ana bukatar yin babban aiki ne tsakanin bangaren zartaswa da majalisa, ta yadda za a yi zube ban kwaryata na kundin tsari domin a yi mishi kwaskwarima. Abin a gode wa Allah ne cewa a majalisar dattawa da ta dokoki gabadaya shugabancinsu na hannun ‘yan jam’iyyar shugaban kasa ne, wanda hakan zai taimaka wurin aikata abin da ake muradi.
Kamar yadda ya kasance dan kasa na gari tun zamanin soji, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya na ci gaba da jaddadawa ‘yan kasa a ciki da wajen Nijeriya cewa za su yi alfahari da gwamnatinsa a 2023 karshen wa’adin mulkinsa. Duk da haka ba zai yiwu wasu baragurbi su tilasta shi wurin daukar matakin da ba shi ba, wanda karshenta ba zai haifar da da mai ido ba.
Ai raini ne da rashin hankali ma a ce wai wasu sun ba Shugaban Kasa wa’adin da idan bai daidaita fasali ba, kasar za ta fashe. Wannan barazana ga hadin kan Nijeriya daga wasu tsiraru ba abin da za a lamunta ba ne. Abin takaicin ma wai suna bayar da irin wannan wa’adin ne a daidai lokacin da kasar ke farfadowa daga annobar Korona.
Kokarin kawo abubuwan da za su dauke hankalin Shugaban Kasa a irin wannan lokaci ba karamin rashin hankali ba ne da nuna rashin kishin kasa a daidai lokacin da gabadaya kasashen duniya ke fafutukar neman mafita.
Ya kamata masu wannan yekuwa tare da ba da wa’adi su fahimci cewa fa Nijeriya kasa ce da ke da mutum sama da miliyan 200. Ra’ayinsu ba komi ba ne face digon ruwa a teku, don haka su bar ‘yan kasa su bayyana abin da su ke so, ba su rika kokarin yin karfa-karfa ba.
Ba ma sai an fada wa mutum ba, wadannan makiyan Nijeriya ne, su ke kokarin kawo sabani da rikici a kasar. So suke su ga komi ya rushe don muguwar bukatarsu ta biya.
Ire-irenmu da suka fahimci halin da a ke ciki, da kuma irin matakan da kasashen da suka ci gaba suka dauka irinsu Amurka, Rasha da sauransu, mun san yadda ake gudanar da nagartacciyar gwamnati da hanyoyin da ake bi.
Tun bayan da Kungiyar Kwadago ta janye batun yajin aiki da zanga-zangarta makon da ya gabata, bayan da suka fahimci hakikanin gskiya dangane da krin kudin man fetur tare da yin sulhu kan batun karin kudin wutar lantarki, wasu abin bai musu dadi ba, sai suka koma shirya bita-da-kulli ga gwamnati.
Yekuwar da Kungiyoyin AFenifere, Ohanaze Ndigbo da PANDEF suke yi tana kan hanya, amma dole ne su rika bin hanyoyin da suka dace wurin neman abin da suke so, don kar su aikata abin da zai tba mutunci da hadin kan Nijeriya.
Su kuma jam’iyyun adawa da suke fakewa da masu yekuwar daidaita fasalin kasa don su rusa gwamnati, ya kamata su sani cewa, suna ci gaba da kasancewa jam’iyya ne saboda akwai gwmanatin a kasar.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya riga ya kafa misali na yadda ake gudanar da gwmanati mai nagarata. Babban abin da ya ke bukata a yanzu shi ne hadin kai daga gabadaya al’ummar Nijeriya domin ya kai ga nasara.
Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa
Share.

About Author

Leave A Reply