Buhari Ya Jinjinawa ‘Yan Kwallon Kwando Mata

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa tawagar mata ‘yan kwallon kwando ta kasar, D’Tigress, saboda samun gurbin cancantar shiga gasar Olympics ta mata da za a yi a birnin Tokyo a 2020.

Shugaban ya bayyana jin dadinsa kan nasarar da suka samu a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin da yammaci.

Ya nemi ‘yan tawagar kwallon kwandon su ci gaba da jajircewa sannan su fitar da kasar kunya a wurin gasar.

Share.

About Author

Leave A Reply