Buhari Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Rungumi Allurar Rigakafin Cutar Korona

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci dukkan ‘yan Nijeriya da suka cancanta da su karbi allurar rigakafin cutar korona da aka fara bayarwa a fadin kasar nan a halin yanzu, “Don ta haka ne zamu kare kanmu daga kwayoyin cutar.”

Shugaba Bujari yana jawabi ne bayan da aka yi masa allura a Abuja, ya ce, “Na karbi allurar a karo na farko kuma ina umartar dukkan ‘yan Nijeriya da suka cancanta da su gaggauta karbar allurar don kare kansu daga kwayoyin cutar.”

Ya kuma bukaci dukkan gwmanonin kasar nan da sarakunan gargajiya da su jagoranci fadakarwa tare gangamin yin allurar a yankin su.

‘“Allura rigakafin ya bamu fatan ganin kasar mu ta kubuta daga cutar gaba daya.

‘“Ina kira ga al’ummma musamman wadanda suka cancanta kamar yadda hukuma ta tsara dasu je wuraren da aka tsara na yin rigakafin don su karbi allurar,’’ inji shi.

Shugaba Buhari ya kuma taya kwamitin kula da cutar korona ta kasa (PTF) murna akan yadda suka tafiyar da lamarin korona a kasar na tun farkon bullar annobar.

Buhari da Osinbajo sun karbi allurar ne ana nunawa a gigajen talabijin na kasar kai staye, gobe kuma za a fara yi wa ma’aikatan lafiya allurer, kamar dai yadda aka tsara.

Babban likitan shugaban kasa, Dr Sanusi Raafindadi ya masa allurar yayin da kuma likitan mataimakin shugaban kasa Dr Nicholas Audifferen ya yi wa mataimakn shugaban kasa Osinbajo.

 

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply