Buhari, ‘Yan Kwadago Da Hayaniyar Karin Kudin Wuta Da Man Fetur, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A makonnin baya, Nijeriya ta cika da korafi kan karin kudin man fetur da wutar lantarki. Kungiyar Kwadagota Nijeriya (NLC), Kungiyar ‘Yan Kasuwa ta Kasa, Jam’iyyar PDP da wasu Kungiyoyin fararen hula sun nuna damuwa kan lamarin. Sai dai a gabadaya lamarin, batutuwan da suke yi babu wata kwakkwarar hujja da suke bijirowa da ita.

Akwai wata dadaddiyar magana da ke cewa: “Yara ashirin ba za su iya yin wasa na shekara 20 ba.” Matakin da Gwamnati ta dauka na karin kudin man fetur ya biyo bayan cire tallafin mai da Gwamnatin ta yi ne.

A tarihin harkar man fetur na Nijeriya, kudin tallafi da ake warkewa, ya fi komi lakume wa gwamnati kudade, kuma ya ke hana ta gudanar da muhimman ayyukan raya kasa irin wannan tallafi a tsawon shekaru. Saboda kudaden da ya kamata a yi wadannan ayyukan da su, da su ne ake bada tallafin man fetur din. Wanda sam ba ya taimakawa talakawa

An cimma matsaya kan rashin dacewar ci gaba da bayar da tallafin man fetur. Kawai an rasa wacce gwamnati ce za ta rufe ido ta cire tallafin. Idan har Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rufe ido ya fuskanci kalubalen manyan mutanen da suke cikin harkar man fetur a Nijeriya, ya cire tallafi, toh mene ne zai sa kungiyar kwadago ta NLC da TUC za su dau zafi haka, alhali lamari ne da ya shafi harkar man fetur.

Ya na da kyau ýan Nijeriya su kwana da sanin cewa daga cikin ajandodin jamíyyar APC tun kafin ta shiga ofis a shekarar 2015 akwai batun yi wa sashen man fetur garanbawul. Amma tun wannan lokacin, shugaba buhari ya yi mursisi da ido daga dukkan wani matsi wurin daidaita farashin man fetur. Wanda sai a nan gaba ne za a ci moriyar abin.

Abin dadi a gabadaya lamarin shi ne wasu masu ruwa da tsaki wadanda suka san me suke yi a harkar man fetur irinsu kungiyar MOMAN da sauransu sun jinjinawa wannan mataki na shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cire tallafin man fetur, domin sun san amfaninshi na da matukar yawa ga ci gaban Nijeriya.

Kungiyar masu ruwa da tsaki a harkar man fetur ta MOMAN a wani ziyara da ta kai wa Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari sun ce wannan cire tallafin da aka yi zai taimakawa Nijeriya wurin farfado da martabar sashin man fetur da kasuwar mai a kasar.

Idan har gwamnati ce za ta ci gaba da ayyana kudin litar man fetur, a bayyane yake cewa ba za a iya janyo hankalin ýan kasuwa masu son zuba hannun jari ba sai ta wannan hanya.

Idan gwamnati ta zare hannunta daga harkar litar fetur din, masu zuba hannun jari za su shigo su gina matatun man fetur, saboda tabbas za su samu riba mai tarin yawa. Wannan abin da Shugaba Buhari ya yi zai sa a samu yawaitar matatun man fetur, daga nan za a samu yawaitar man fetur din wanda zai tilasta dole a samu faduwar kudin lita. Wannan kuma zai sa a rage shigo da tataccen man fetur.

Ba zai yiwu a ce gabadaya manufar kungiyar kwadago babu na tsinta ba, amma dai ba su bi hanyar da ta dace ba. Domin dole ne a sadaukar da jin dadi na dan wani lokaci kafin a kai ga nasarar da ake tsammani.

Kafin zuwan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kowa ya san irin bakar azabar da ýan Nijeriya suka tsinci kawunansu a bin layin shan fetur, masu ababen hawan sun sha kwana a gidajen mai, matafiya sun yi ta yin balaguro da galan din mai a motocinsu. Wanda a sanadiyyar haka dubbai sun mutu. Duk ba su kalli irin kokarin da Buhari ya yi ba wurin kawo karshen wannan lamari.

Shi kuwa batun wutar lantarki, sam babu hannun shugaban kasa Buhari, domin kuwa tuni aka sayar da bangaren wutar lantarkin, a hannun ýan kasuwa take. An fara yunkurin sayar da bangaren lantarki ne tun zamanin gwamnatin Janar Babangida a 1988.

Shekara 10 bayan nan ne Janar Abdussalami Abubakar ya aiwatar da wannan kudurin a shekarar 1999 inda aka sayar da NEPA wacce daga bisani ta koma PHCN. A shekarar 2013 ne aka kammala sayar da kamfanin PHCN lokacin da Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ya mikawa kamfanonin da suka sayi PHCN din.

Tambayar a nan ita ce, ko me ya sa kungiyar kwadago da PDP suke kokarin rudar da mutane? Ta yaya za su zargi Buhari da karin kudin wutar lantarki? Su manta cewa a zamanin gwamnatin rashawa ta PDP ne aka sayar da kamfanin wuta na PHCN din? Su dama PDP suna yin wannan soki burutsun ne da gangan da zimmar bakanta gwamnatin Buhari.

A gabadaya zancen karin kudin mai da wuta, su masu ruwa da tsaki a harkar man fetur din, wadanda saboda tsaba son rai su ne suke rikitarwa tare da ruda mutane don kar su fahimci hakikanin manufar gwamnatin Buhari a yakin da take yi da cin hanci da rashawar da ke addabar bangaren man fetur din Nijeriya.

A nawa fahimtar da tunanin shi ne a daina biyan tallafi ga man fetur da wutar lantarki, a maimakon haka a mayar da tallafin ga harkar ilimi, lafiya, da raya kasa da tallafi ga talakawa. A aikin hankali, wannan shi ne abin da ya kamata duk wata gwamnati da ta san abin da ke gabanta ya kamata ta yi. Ba ta tsaya wani abu wai shi tallafi ya yi ta dakile kokarinta ba.

Kungiyar Kwadago ta NLC da TUC da dukkanin masu biye musu ya kamata su sa hankali a wannan lamari nasu. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba shi da wata boyayyiyar manufa da yake da ita face kokarin da yake ta faman yi na ganin ya gyara Nijeriya. Ya dade yana nuna irin nagatarsa da kishin kasa. Abin da ake bukata shi ne a ba shi hadin kai wurin cimma burinsa.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).

 

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply