Cikin Kwanciyar Hankali Za A Yi Zabe A Edo, Cewar ‘Yan Sanda Ga Mazauna Jihar

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Jami’an tsaro a Edo ranar Lahadi sun jadadda wa mazauna Edo aniyarsu ta tabbatar da an yi zaben gwamna ranar 19 ga watan Satumba cikin kwanciyar hankali.

Sun bada tabbacin ne yayin wani taron ‘Tauna aya don tsakuwa ta ji tsoro’, da gamayyar jami’an tsaron suka yi na kwana biyu a jihar.

SP Chidi Nwabuzor, Kakakin rundunar ‘yan sanda reshen Edo wanda ya yi wa manema labarai jawabi ya bada tabbacin hakan ya zama wajibi ne don kawar da tsoro a zukatan masu kada kuri’a.

Nwabuzor ya ce saboda saura kwanaki shida ya rage a yi zaben, hankula na ci gaba da tashi, hakan ne ya wajabta dalilin karfafa mazauna jihar.

Ya bukaci mazauna jihar da su da su sani cewa aikin kare su na ga jami’an tsaro ne, yana mai cewa su fito ranar Asabar don zaben dan takarar da suke so.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gamayyar jami’an tsaron da suka fito atisayen sun gada Sojoji, ‘yan sanda, kwastan da jami’an tsaron farin kaya.

Sauran sun hada da Hukumar kare fararen hula, Rundunar sojojin sama, Hukumar kiyaye hadurra ta kasa, Hukumar kula da ‘yan fursuna, Hukumar kula da shige-da-fice ta kasa da kuma Hukumar yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

 

Share.

About Author

Leave A Reply