Coronavirus: Makarantu A Jihar Kano Sun Bi Umurnin Gwamnati

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Makarantu a wasu sassan jihar Kano sun bi umurnin Gwamnatin jiha na rufe duk cibiyoyin ilimi da ke jihar domin kare yaduwar cutar COVID-19.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya, NAN, ta ruwaito cewa duk makarantun da ta kai ziyara a cikin birnin Kano a rufe su ke, sai dai wasu mutane daidaiku da aka gani a harabar makarantun.

A cikin makarantun Kawaji Boys Secondary School, Day Science da Lufaloy Schools kuwa wasu tsirarun malamai aka gani suna tattaunawa.

A makarantun Rumfa College, Bennie International School, Intercontinental da Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kano su kuma, wasu masu gadi aka gani da wasu jama’a kadan.

NAN ta kara da cewa, ta hadu wasu mutane kadan a cikin Jami’ar Bayero da Jami’ar Maitama Sule da ke cikin babban birnin jihar.

Idan ba a manta ba, a ci gaba na matakan da ta ke dauka na kare yaduwar COVID-19 a jihar, Gwamnatin jihar ta yi umurnin rufe makarantun firamare, sakandare da na gaba da sakandare.

Share.

About Author

Leave A Reply