Da Yiwuwar APC Ta Bai Wa Dan Kabilar Ibo Takara Cewar Daraktan VON

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daraktan kafan watsa labarai na ‘Voice of Nigeria’, VON, Osita Okechukwu, ya ce akwai yiwuwar a shekarar 2023 jam’iyyar APC ta bai wa dan Kudu maso yammacin kasar takara.

Okechukwu ya bayyana haka ne a wajen taron jam’iyyar da aka yi a Sakatariyarta da ke Inugu a ci gaba da shirye-shiryen da take na tunkarar zaben maye gurbi ranar 31 ga watan Oktoba.

Ya yi nuni da cewa bai wa dan kabilar Ibo kujerar zai tabbatar da adalci ne da daidaito kamar yadda yake a kundin tsarin mulki na jam’iyyar.

Shugaban VON din ya yi nuni da cewa idan aka zabi dan kabilar Ibo a matsayin shugaban kasa za a samu bunkasar harkokin kasuwanci a kasar.

Osita Okechukwu, ya kuma jinjina wa jam’iyyar a matakin jiha kan kokarin hada kan ‘ya’yanta da ta yi, irinsu da Cif Adolphus Ude, Queen Nwankwo da sauransu.

Tsohon mataimakin Shugaban jam’iyyar yankin Kudu maso gabas, Cif Emma Eneukwu, ya nuna farin cikinsa kan sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar da aka yi.

Eneukwu also urged for unity of purpose to make the party win the upcoming state constituency bye-election and other elections in 2023. Eneukwu ya kuma bukaci a sake hadin hadin kai kan zaben maye gurbin da ke tunkaro jihar da ma zaben 2023.

Zaman ya samu halartar shugabannin jam’iyyar daga gundumomi 260 na jihar.

 

Share.

About Author

Leave A Reply