Dabi’a Mara Kyau Daga Wasu Mahukuntan Jam’iyyar APC Ta Jihar Kano

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Usman Suleiman Sarki
Mulkin dimokaradiyya tsari ne da ya ba al’ummar kasa damar samar da shugabanni da suka aminta dasu don kawo musu ci gaba da kyautatuwar rayuwa. Hakan ya bada dama na kafa Jam’iyyu da zasu zamo matattakalar hawa kujerun mulki daban daban da ake da su kuma hakan ya ba mutane damar shiga dukkan jam’iyyar da ta yi daidai da ra’ayinsu.
A tsarin dimokaradiyya bambancin ra’ayi ko Jam’iyya bai bayar da damar cin zarafi ko yin gaba da juna ba, domin a lokuta da dama a kan iya samun chanjin ra’ayi ko Jam’iyya inda mutane dake da wadannan bambance-bambance ke haduwa a cikin ra’ayi ko Jam’iyya daya. Babban abin takaici da damuwa a siyasar Jihar Kano a yau shine yadda ake tafiyar da ita ba tare da girmamawa da mutunta juna ba musamman a tsarin Jam’iyyu masu adawa da juna a wasu lokuta ma a kan samu irin wannan matsalar a cikin Jam’iyya guda.
Jam’iyyar APC ita ce Jam’iyya mai mulki a jihar Kano, wacce ita ya dace ta zamo fitila wajen haskawa gwamnati hanyar kyautata al’amura da samar da ci gaba a jihar, amma abin takaici shi ne yadda shugabanni da wasu masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar suka maida siyasa a matsayin hanyar cin mutunci da cin zarafin junansu dama yan adawa wanda hakan ba dai dai bane kuma bazai haifar mana da komai ba face koma baya da haddasa fitintinu a tsakanin al’umma.

Ya zama wajibi mu yi jan hankali da kuma kira ga Mai Girma Gwamna, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ya tashi tsaye kuma ya tsawatar wa da wadannan mutane masu kokarin mayar da siyasa a matsayin tsari na cin zarafi da mutuncin mutane domin hakan yana bata sunan Jihar Kano dama Arewacin Nijeriya baki daya.
A karshe ina kira ga yan uwana matasa da mu guji yin biyayya ga duk wanda zai ingizamu mu aikata wani abu mara ma’ana ko kokarin yin amfani damu don cin mutuncin wani saboda bambancin ra’ayi ko Jam’iyya.
Allah ya taimaki jihar Kano da Nijeriya baki daya, ya kara mana lafiya da zaman Lafiya.
Usman Suleiman Sarki
08058330007

Share.

About Author

Leave A Reply