Dalilin Da Ya Sa Zamu Saya Wa Hon. Kaitafi Fam Don Takara- Matasan Bade/Jakusko

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Biyo bayan kiran da matasan kananan hukumomin Bade/ Jakusko a jihar Yobe su ka yi na bukatar hadimin shugaban majalisar dattawan Nijeriya (SA Protocol)- Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya fito takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya, wandan ya jawo a makonin da suka gabata hadimin ajiye mukamin shi, kamar yadda doka ta tanada, tare da bayyana gamsuwarsa kan wannan bukata ta al’ummar yankin.

A wannan makon uwar jam’iyyar APC ta kasa ta shelanta fara sayar da fam ga yan takara a kowane mataki na neman tsaya wa takara, wanda ganin haka keda wuya, matasan suka saka bukaci matashin dan siyasar; Hon. Kaitafi da cewa sun hutar dashi kan sha’anin sayen fam din tsayarsa takara, dawainiyar yakin neman zabe da makamantan su, inda nan take suka ayyana bude asusun karo-karo a tsakanin su don tara kudin da zasu masa fam din takarar kujerar majalisar wakilai a zaben 2023 mai zuwa- yayin da zancen da ake yanzu tafiya tayi nisa.

Wakilinmu ya gano cewa wannan mataki da matasan suka dauka shi ne irinsa na farko a tarihin siyasar yankin, sannan kuma hakan yana zama yar manuniya dangane da farin-jinin Hon. Kaitafi a zukatan al’ummar yankin, haka kuma sako ne mai cike da armashi kan irin yadda matasan ke hankoron samun kyakkyawan wakilci a zauren majalisar wakilan wanda suka sha korafi kan halin ko-in-kula da wasu masu rike da madahun iko ke nuna wa matasa tare da zarge-zargen rashin tabuka abin azo a gani da wasu yan siyasa a yanki ke yi.

Bugu da kari, wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban asusun tattara kudaden, Alhaji B. Muhammad Gashuwa, inda ya warware zare da abawa kan sha’anin tare da bayyana cewa, “Alhamdulillah, wannan hadaka ce ta jam’iyyun siyasa daban-daban masu kishin ci gaban wannnan yanki, inda muka hadu kuma mu ka bukaci Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya fito takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya, domin ya wakilci wadannan kananan hukumomi namu. Kuma kasancewar ya amsa wannan kira namu, bayan ya nemi izinin Gwamnan jihar Yobe da uban-gidan shi, shugaban majalisar Dattawan Nijeriya tare da sanya masa albarka shi ne muka ga ya dace mu da kanmu mu tara kudaden da za a kashe a takarar.”

“Shi ne muka shiga mu ka zauna don tsara yadda al’amarin zai gudana ta fannin yin rijista da hukumar ‘Cooperate Affairs’, hukumar kula da biyan haraji ta gwamnatin tarayya (FRIS) tare da duk bangarorin da abin ya shafa a karamar hukumar Bade a jihar Yobe, wanda a karshe muka bude wannan asusun ajiya na banki. Wanda ta wannan tallafin da jama’a zasu saka a asusun za mu saya masa fam din takara, kuma mu yi zirga-zurgar yakin neman zabe da sauran abubuwan da takarar ta kunsa; in sha Allah.”

“Haka kuma, yanzu haka zancen da muke da kai, kasa da awanni 24 da bude wannan asusun mun samu sama da naira miliyan biyu. Sannan kudirin da muke dashi kan haka shi ne a matsayin Alhaji Sani Kaitafi mai taimakon al’umma, koda mun samu sama da mikiyan 100 ba zai zama damuwa ba ganin cewa wadanda suka kafa wannan gidauniyar mutanen ne masu kwatamta adalci da sanin yakama, za mu yi amfani da sauran kudin da suka rage bayan kammala dawainiyar zabe; wajen raba su ga mabukata a cikin al’ummar mu. Saboda ba ma son Hon. Ahmed Kaitafi ya saka sisin-kwabon sa a tsayawa takarar sa a Bade/Jakusko. Kuma hatta zuwa wajen sayen fam a ofishin uwar jam’iyyar APC mun dauke masa, mu ne zamu je mu saya sannan mu mika masa.”

Shugaban ya kara da cewa, wannan hadaka ce wadda ta shafi kowane bangare na al’ummar wannan yanki; matasa maza da mata tare da manyan dattijanmu da shahararrun duk masu fada aji a wadannan kananan hukumomi, su ne suka bayyana matashin a matsayin nagartaccen wakilin da za su damka masa amanarsu. Ya kara da cewa, “kuma ba haka kawai muka yanke wannan hukunci ba, sai da kowane bangare ya dora al’amarin a mizanin hankali tare da hangen nesa dangane da cancanta. Kuma ko shakka babu jama’a a shirye suke wajen bai wa wannan hadaka cikakken goyon baya.”

“Daya daga cikin abin da kowa ya yi musharaka bisa ga nagartar Hon. Kaitafi shi ne jajjirtacen matashi ne mai matikar kishin al’ummar wannan yanki, kuma hakan ya bayyana ta la’akari da yawan dawainiyar da yake yi wa jama’a alhalin ba ya rike da wata kujerar siyasa da aka zabe shi. Wanda ta wannan jama’a suka yi hasashen cewa, a halin da ake ciki, idan mutum irin sa zai yi haka, to ina ga idan an bashi cikakkiyar damar wakilcin yankin a zauren majalisar wakilai. Sannan mutum ne mai ladabi da biyayya a zamansa karkashin mai gidansa, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan.”

A nashi bangaren kuma, Babban Sakataren asusun tattara kudaden, Nasiru Alhaji Auwal Mai-manja ya bayyana cewa, a matsayin su na matasa kuma masu kishin yankin, shi ne suka yanke shawarar samar da asusun; ba tare da masaniyar Hon. Sani Ahmed Kaitafi ba. Sannan ya sanar da cewa, hakan ne ta dalilin nagartar da yake da ita tare da dimbin alhairan da ya shuka wa jama’ar wadannan kananan hukumomi na Bade da Jakusuko- al’amarin da babu wanda zai musanta hakan.

“Kadan daga cikin abubuwan alhairan da ya aiwatar don inganta rayuwar al’ummar mu sun hada da bayar da tallafi a fannin ilimi- biya wa dalibai kudin karatu, sayen littafai, kayan karatu, kwamfotoci ga dalibai. Gina rijiyoyin burtsatse a wurare daban-daban, tallafin gina masallatan Jummu’a kimanin biyar, bai wa mata sama da 200 jari da yan kasuwa da sauran su. Sannan na san ya bayar da kyautar motoci ga jama’a sama da 15 cikin kasa ga watanni biyu. Sannan da tallafi a harkar noma da kiwon lafiya.”

Share.

About Author

Leave A Reply