Duniya Ko Masana’antar Ƙera Mutane?

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Umar Shuaibu

Ba abin mamaki ba ne idan mutum ya ce akwai masana’antu daban-daban a cikin wannan duniyar tamu da suka kware wurin ƙera abubuwa daban-daban da muke amfani da su a yau da kullum.

Ba zan yi magana ba ne akan yadda masana’antu ke ƙera abubuwa saboda wannan rubutun bai da dangantaka ta ƙut da ƙut da wannan ɓangaren, abinda zan maida hankali akan shi shi ne yadda abubuwan da aka ƙera ke rayuwar su.

Misali, idan muka yi dubi zuwa ga rayuwar Mota, wanda yana ɗaya daga cikin abubuwan da ake ƙerawa a wannan duniya, za mu ga cewa ana kammala ƙera ta za a sa ta a kasuwa, wani mutum ya saye ta, ya yi ta amfani da ita har ranar da za ta buga, ya zama bata da amfani sai a kai ta bola.

Haka idan muka duba sauran abubuwan da ake ƙerawa a masana’antu suma haka rayuwarsu ke kasancewa.

Mu dawo zuwa ga rayuwar mutum wanda shi ke ƙera motoci da sauran abubuwa. Rayuwar mutum a yau ta fara kamanceceniya da rayuwar abubuwan da masana’antu ke ƙerawa. Domin da yawan mutane a yanzu ba su ma san menene manufar halittar su ba, ba su san waye su ba. Suna wayan gari ne kawai su gan su a matsayin mutane, su rayu a matsayin kayan aikin wasu (ba tare da ma sun sani ba) su mutu a je a binne su, shikenan.

Da yawa daga cikin mutane a yau ba su san waye su ba, wasu kuma sun manta. Misali idan zaka tambayi da yawa cewa; waye su? Za su bada amsoshi mabanbanta, wani zai amsa da cewa shi Likita ne, wani yace Shi Malami ne, wani yace shi Ɗan Jarida ne da sauran su. Inda zaka sake tambayar su kafin ka zama Likita kai waye ne? Zai amsa da cewa shi Ɗan makaranta ne. Saboda mutane sun koma martaba sana’a fiye da ɗan Adam.

Idan muka duba rayuwar mutum a yau daga Haihuwa zuwa mutuwa za mu ga cewa ita ma ta fara kama da irin ta ƙerarrun abubuwa. Alaƙar dake tsakanin ma’aikata da masu ɗaukan su aiki a kamfanoni da masana’antu ta koma irin alaƙar dake tsakanin Mota da wanda ya saye ta. Sam babu ɗan Adamtaka a cikin ta. Ma’aikaci na da muhimmanci ne matukar yana karfi ko ƙwaƙwalwa da zai yiwa kamfani aiki, duk ranar da amfanin shi ya kare ko kuma kamfani ya samu wanda ya fi shi haka zata kore shi ta dauko wani ma’aikacin.

Ba anan kaɗai matsalar ta tsaya ba, akwai binciken da ya tabbatar da cewa hatta tunani, al’adu da hanyar rayuwar da yawan mutane a yau wasu mutane ne suka tsara shi ta yadda zai amfane su. Kuma tunda ba kai tsaye ake zuwa a tsara wa mutane wadannan abubuwan ba, fahimtar hakan yana yiwa mutane da yawa wahala. Amma idan muka duba cikin nitsuwa za mu iya ganin tasirin wadannan tsare-tsaren a cikin rayuwarmu ta yau da kullum.
Misali, tausayi da son juna na raguwa a cikin al’umma, taimakon juna yayi karanci a cikin mutane, kowa ta kanshi yake yi, ba ruwan makwabci da makwacin shi.
Kuma a ‘yan shekarun baya kaɗan lamarin ba haka yake ba.

Wannan shi ya maida da yawan mutane a yau kayan aikin wasu mutane ba tare da ma sun sani ba.
Irin wadannan mutane za mu iya cewa ba su da bambanci da abubuwan da masana’antu ke ƙerawa, domin su ma suna kare rayuwan su ne ba tare da sun amfani kan su da komai ba ko da kuwa sun mallaki gidaje da motoci da manyan masana’antu a lokacin rayuwar su.

Umar Shuaibu.
umardusha@gmail.com.
29/04/2021.

Share.

About Author

Leave A Reply