EFCC Ta Fara Bincikar Wata Jiha Saboda Badaqalar Naira Biliyan 5

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban hukumar yaqi da cin hanci ta qasa EFCC, Mista Abdulrashid Bawa, ya ce hukumar ta fara bincikar wata jiha bisa zargin badakalar naira biliyan 5.

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin taron ganawa da manema labarai da fadar shugaban qasa ta shirya ranar Alhamis, a Abuja.

Wannan na xai daga cikin alfanun samar da sabon  vangaren leqen asiri da bincike na hukumar  ne , in ji shi.

Shugaban, wanda ya qi aminceewa da bayyana sunan jihar don kaucewa tuggu da surkullen kafafen yaxa labarai, ya ce hukumar za ta ci gaba da anfani da binciken sirri don gano badakala da almundahana a faxin qasar.

Da ya ke amsa tambaya kan saqonnin barazana da ya ke samu daga mutane. Shuganban ya ce ya sanar da shugabn rundunar ýan sanda kan lamarin ta wayar tarho, sufeta Alkali Baba Usman. Ya kuma ce zai rubuta masa wasiqa kamar yadda aka nema ya yi.

Dangane da ayukkan danfara ta intanet, ya ce hukumar ta samu nasarar cafke ýan dafara 1,502 daga watan Janairun wannan shekarar zuwa yanzu, inda ya koka da cewa, harkar danfarar na qara lalata qimar Najeriya a idon duniya.

Ya bayyana cewar, hukumar na kan shirin samar da vangaren yaqi da danfara domin ganin sun daqile lamarin  Najeriya

Share.

About Author

Leave A Reply