EFCC Ta Kama Masu Laifi 173 Ta Kuma Kwato Naira Miliyan 149 A Kano

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar EFCC reshen jihar Kano ta samu nasarar cafke masu laifi daban daban har mutum 173 a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu na wananan shekarar.

Shugaban hukumar na yankin Kano, Mr Mualledi Farouk-Dogondaji, ya bayyana haka tattaunawarsa da manema labarai a Kano ranar Asabar, ya kuma ce, wadanda aka kama sun aiki laifukkan da suka hada ne da badakalar kudade da kuma laifikkan da suka hada da na zamba ta kwamfuta.

Wasu kuma da aka kama sun aikata laifin zamba ciki aminci ne da kuma kasu damfara al’umma da sunan adashin gata.

Ya kuka bayyana cewa, hukumar ta sau nasarar karbe kudi da suka kai Naira Miliyan 149 daga hanun wadanda ake zargin daban-daban a cikn wannan lokacin an kuma samu nasarar sanun hukuncin dauri ga wasu mutum 11.

Ya kuma shawarci al’umma su guji hulda da ‘yan damfara su kuma kai wa hukumar bayanai masu mahimmanci wadanda za su kai ga dakile ayyukan masu damfara a jihar gaba daya.

Farouk-Dogondaji ya kuma ce, wannan kiran ya zama dole don kuwa da taimakon bayanai daga al’umma ne suka samu nasarorin da suke alfahari dasu a hali yanzu.

 

Share.

About Author

Leave A Reply