El- Rufai Ya Nemi Musulmi Su Yi Koyi Da Darussan Da Ke Tattare Da Babbar Sallah

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nemi al’umma musulmi su yi koyi da dukkan darussosin da ke tattatare da bukukuwan babbar sallah tare da kuma yi wa kasa addu’a na fita daga mawuyacin halin da kasar ke ciki, ya kuma nemi a kara kula da daukar matakin kariya daga cutar korona.

Gwamna na Kaduna ya bayyana haka ne a sakonsa na babbar sallah, ya kuma nemi Muslmai su tabbatar da koyi da darussaan da sadaukauwar babbar sallah ke koyarwa.

Ya kuma yaba wa al’ummar jihar akan yadda suka jure matsalolin da ake fama dasu a wanann lokacin.

Gwamna ya kuma nemi al’ummun jihar su hada kai a kokarin ganin an samu zaman lafiya a sassan jihar, ya kuma nemi su taimaka wa jami’an tsaro a kokarin da suke yi na kawo karshen matsalar.

Share.

About Author

Leave A Reply