Fafaroma Francis Ya Yi Allah Wadai Da Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Ta’adda

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Umar Shu’aibu

Fafaroma Francis ya yi Allah wadai da masu ƙera makamai da masu safarar su zuwa ga ‘yan ta’adda.

Fafaroma ya yi wannan tofin Allah wadai ne a yau Laraba 10 ga watan Maris 2021 a lokacin da yake bayani dangane da ziyaran da ya kai kasar Iraqi.

Ya bayyana cewa abin farin ciki ne matuka da ya kasance shine fafaroma na farko da ya gabatar da irin wannan ziyaran, ya kuma bayyana ziyaran sa a wannan lokaci da Duniya ke fama da annobar Korona a matsayin fata ga Kiristoci da Musulmi Bayan kwashe shekaru suna fama da yaƙi da ta’addanci.

A wani zantawa da ya saba gabatarwa kowace Laraba, Fafaroma ya ce: “Mutanen Iraqi na da ikon rayuwa cikin aminci da kuma damar sake farfaɗo da kiman su.”

Ƙasar Iraqi na fama matsalolin cin hanci da rashawa da kuma yawaitan hare-hare tun bayan shekaru 18 da mamayar da Ƙasar Amurka ta musu.

A ranar Lahadi 7 ga watan Maris, Fafaroma ya kai ziyaran gani da ido a garin Mosul dake arewacin Iraqi inda yaga gidaje da cocin da aka lalata bayan da kungiyar ISIS ta kwace ikon garin tun daga shekarar 2014 zuwa 2017.

Fafaroma ya ƙara da cewa: “Kuma na tambayi kaina (a lokacin ziyaran), ‘wa ke sayar wa ‘yan ta’adda da makamai?, Wa ke sayar wa ‘yan ta’adda makamai a yau da suke gabatar da kisan kiyashi a ko ina, misali a Afrika?”.

“Wannan tambaya ce da nake so wani ya amsa min.”

Fafaroma ya taɓa furta cewa, masu ƙera makamai da masu safarar su za su amsa tambayoyi a gaban Allah watarana.

Yayin da yake ƙira zuwa ga ‘yan uwantaka tsakanin al’ummar Duniya, fafaroma ya bayyana zantawa da yayi da ɗaya daga cikin manyan malaman Shi’a na Duniya Ayatullah Ali Al-Sistani a birnin Najaf a matsayin ganawan da ba zai taɓa mantawa da shi ba.

Kiristocin Iraqi na ɗaya daga cikin kiristocin da suka fi jimawa a Duniya, adadin su ya ragu zuwa dubu 300 maimakon adadin miliyan daya da dubu dari biyar da suke kafin mamayar Amurka da kuma hare-haren ‘yan kungiyar ISIS.

Share.

About Author

Leave A Reply