Farashin Hatsi Ya Sauka Da Kashi 25 A Yobe

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Farashin hatsi ya ragu da kusan kashi 25 a kasuwannin da ke cikin Damaturu, fadar jihar Yobe.

Rahotanni sun nuna cewa ranar Talata buhun masara da ake sayarwa naira 20,000 makonni biyu da suka wuce ya dawo naira 16,000 yayin da gero shi ma ya sauko zuwa naira 14,000 daga 20,000.

Sai dai rahotannin sun tabbatar da cewa dawa da wake har yanzu suna kan farashinsu na 20,000 a tsawon lokacin nan.

Da aka tuntubeshi, Shugaban masu sayar da hatsi a kasuwar Lahadi a Damaturu, Alhaji Ibrahim Yusuf, ya alakanta saukar kayan da samun sabbin kaya a kasuwar.

“Farashin masara da gero ya sauka saboda yanzu sabon kaya ya shigo kasuwa.

“Sai dai na wake da dawa yana nan yadda ya ke, saboda sabbin  kaya basu shigo ba,” inji Yusuf.

Sai dai, ya roki gwamnatin Yobe da ta tallafa wa kananan ‘yan kasuwa da bashi mara tsanani, sannan kuma ta kammala Kasuwar zamani ta Damaturu a kan lokaci.

“Mun dade muna kasuwanci a wannan kasuwar ta Kasuwar Lahadi, wacce jihar Yobe ta kafa kusan shekaru 30 da suka gabata.

“A tsawon shekarun nan kasuwar na fuskantar matsalar tsaro, ambaliya da sauransu.

“Don haka ne muke kiran gwamnati da ta gaggauta kammala kasuwar don rage mana radadi da kuma bunkasar tattalin arzikin jihar,” inji Shugaban.

 

Share.

About Author

Leave A Reply