Farashin Hatsi Ya Tashi A Kasuwanin Jihar Yobe

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Bincike na musanman da aka gudanar ya nuna cewa, an samu hauhawar farashin kayan abinci a kasuwannin jihar Yobr, musamman a kasuwa hatsi ta garin Potiskum.

Bayanan da aka samu a ranar Litinin ya nuna cewa, farashin kayan abinci musamman wake da shinkafa da masara da dawa da kuma gero duk sun tashi.

Buhun wake da aka sayarwa Naira 30,000 a mako uku da suka wuce a halin yanzu ana sayar dashi Naira 35,000 zuwa N36,000, yayin da ake sayar da tiyan waken wadda aka sayar a Naira 900 mako uku da suka wuce a halin yanzu ana sayar da shi ne a kan Naira 1000 haka kuma ana sayar da bukun shinkafar gida akan Naira 34,000 zuwa 35,000 a mako uku da suka wuce a halin yanzu ana sayar dasi ne a kan Naira 38,000, yayin da kuma ada ake sayar da tiyan shi akan Naira 900 yanzu kuma ya zama Naira 1,000 zuwa Naira 1,100.

Bayanin ya kuma nuna cewa ana sayar da buhun masara a kan Naira 14,000 zuwa Naira 15, 000 a mako uku da suka wuce amma a halin yanzu ana sayarwa ne akan Naira 18, 500 zuwa Naira 19, 000, yayin da kuma ake sayar da tiya akan Naira 500.

Haka kuma ana sayar da buhun dawa akan Naira N13, 000 zuwa Naira 14, 000 a mako uku da suka wuce amma a halin yanzu ana sayar dashi ne akan Naira 16, 500 zuwa Naira 17, 000, yayin da kuma ake sayar da tiya akan Naira 500.

A tsokacinsa, sakataren kungiyar ‘yan kasuwar Potiskum, Alhaji Abdullahi Garundaye, ya dangantar karancin hatsin da ake fuskanta a halin yanzu da mastalar tsaro da ake fuskanta a yankin arewa maso gabas, ya ce a shekakar da ta gaba manoma da dama basu samu yin noma ba saboda farmakin ‘yan bindiga a yankin Borno, akan haka ba a samu abinci yadda ya kamata ba a kasuwaninmu, akan haka ya bukaci gwamnatin jihar Yobe ta kawo dauki na musamman don samar da abinbci a fadon jihar

Share.

About Author

Leave A Reply