Farfesa Bogoro: Murnar Cika Shekara 62 Ga Nagartaccen Masani, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Mutum malalaci ba ya iya tabuka komi a rayuwrasa, shi kuwa mutum mai kifin basira, taka-tsantsan da hangen nesa irin Farfesa Elias Suleiman Bogoro, yana sa dukkan karfinsa da iyawarsa ne wurin ganin ya aikata abin da ya kamata. Babu makawa akan haka ne aka sa shi cikin jerin mutanen da suke aiki babu dare ba rana wurin ganin hakar Shugaba Buhari ta cimma ruwa dangane da bunkasa ilimi.

A wannan lokaci da ya ke cika shekara 62 na rayuwarsa, ina so ya sani cewa mutunci shi ne mutum, duk da ba kowanne mutum ba ne ya kamata a mutunta. Haka kuma a kowanne zamani ana samun mutane da suka fita daban, wadanda ka  iya canza duk wani yanayi. Farfesa Bogoro mutum ne mai dabi’u kyawawa, dattako da kuma sanin ya kamata.

A duk dai wannan buki na cikarsa shekara 62 a duniya, ina rokon Farfesa da ya ci gaba da rayuwa mai nagarta kamar yadda aka sanshi da ita, hatta mu da muke Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC) mun san irin kokarin da yake yi na ganin fannin ilimi ya habbaka a Nijeriya. Ba kawai yana daga cikin managartan da ake da su ba, a’a yana cikin sahun farko.

Ba ya ga irin kokarin da yake yi a Hukumar TETFund wanda ba wannan zan kawo a wannan rubutun na taya murna ba, Farfesa Bogoro ya kasance shahararren masani, wanda ya yi wallafe-wallafe da daman gaske a cikin gida da wajen Nijeriya. Shahararsa ce ta sa ya yi mabambantan ayyuka da Bankin Duniya, UNDP, USAID, DFID, IPCR, OSIWA, NDI, FHI, NACA da kuma IFES.

Farfesa Suleiman Elias Bogoro ya kasance shugaba kuma jagora a tafiyar masana da kuma kwararrun ‘yan boko na cibiyar ‘Think Tank for Translating Research to Innovations, Strategies, Evidence for Policy and National Development’ wacce hedikwatarta ke da matsuguni a Jami’ar Ibadan.

A nijeriyarmu ta yau babu wani da ya yi aiki tukuru kuma aikinsa ya bayyana irin Farfesa Bogoro. A farkon wa’adinsa a hukumar TETFund shi ne ya kawo bincike da bunkasa ilimi wanda daga nan aka samar da sashen na Bincike da bunkasa ilimi a hukumar.

Farfesa Suleiman Bogoro ya samu shaidar karatun digirinsa na farko ne a fannin noma a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1981, ya yi digirinsa na biyu a fannin kimiyyar dabbobi a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya a shekarar 1988, sannan ya tafi Jami’ar ATBU dake Bauchi inda ya yi digirin digirgir a shekarar 1997. An ba shi mukamin Farfesan fannin kimiyyar dabbobi ne a shekarar 2003.

A kokarin cimma burinsa na horas da malaman makarantun gaba da sakandare, TETFund ta samar da wani tsari na horas da wadannan malamai a cikin gida da wajen Nijeriya. Wannan tsarin wanda aka yi wa take da ‘Academic Staff Training and Development (AST&D)’ ya zuwa yanzu ana da malamai 24,194 suna karo ilimi a manyan jami’o’in da ke wajen kasar nan.

Hukumar TETFund a karkashin Farfesa Bogoro ta bayar da gagarumar gudummawa wurin farfado da darajar makarantun gaba da sakandare a Nijeriya, ta hanyar kai agajin gaggawa wurin gine-gine da bunkasa makarantun, tare kuma da bayar da tallafin horo ga malaman makarantun na gaba da sakandare da dai sauransu. Don ganin duk wani aiki na Hukumar TETFund an gudanar da shi bisa ka’ida kuma yadda ya kamata, Farfesa Bogoro ba ya sakaci da bibiyar ayyukan da hukumar ke gudanarwa a fadin Nijeriya, inda yake matsa lamba wurin tabbatar da cewa ayyuka masu nagarta za a gabatar.

Jajircewar Farfesa Bogoro wurin ganin harkar ilimi ta bunkasa wani lamari ne da zai dade a zukata. Kowa na yin riko da aikinsa ne yadda zai iya tafiyarwa. Amma su wadanda ke daukar dawainiyar aikin wasu sun nuna cewa su din nagartattun shugabanni ne.

Kaitsaye ko a fakaice, Farfesa Bogoro zai ci gaba da zama uba, kuma abin koyi ga mutane da dama. Bogoro ya kiyaye mutuncin sunansa ta yadda ya tabbatarwa da duniya cewa, sanya mishi suna irin na Sarki Sulaimanu (King Solomon) bai fadi kasa banza ba. Wani lamari ne da Ubangiji ya kudurta.

Yana kallon duniya ne ta siffar aikata kyakkyawa a kodayaushe. Yana jajantawa wadanda ke halin damuwa da kunci, sannan ya taya murna ga wadanda ke halin farin ciki.

Yadda ake ta zubo sakonnin taya murnar cika shekara 62 ga wannan bawan Allah ya isa ya nuna irin turbar da yake kai. Mutum ne na mutane wanda yake damuwa da damuwarsu.

A daidai wannan lokaci na murna ina fata Farfesa ya ci gaba da kasance mutumin kwarai kuma mai kaunar ci gaba da al’umma. Domin ko ba komi, ita kyakkyawar dabi’a tamkar hayaki ce, ba a iya boyeta.

Addu’armu da fatanmu shi ne bayan wnnan nagartaccen jagora ya kammala wa’adinsa a TETFund a ba shi wata babbar damar da zai yi jagorancin al’umma. Domin ta nan ne kawai za a mori kwarewarsa, kyawwan dabi’unsa.

Barka da zagayowar ranar haihuwa, Farfesa!

– Ibrahim Shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply