Farfesa Gambari A Matsayin Mai Daidaita Lamurra A Fadar Shugaban Kasa, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A lokacin da labarin nadin Farfesa Ibrahim Agboola Gambari a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ya fita, jiya Laraba, kafafen sadarwa, musamman Soshiyal Midiya ta cika da begen wannan zakakuri wanda zai zo ya daidaita lamurra a gwamnatin Buhari.

Zabo Farfesa Gambari a matsayin wanda zai maye gurbin Abba Kyari ya janyowa Shugaban Kasa Buhari yabo da jinjina, ba kawi don irin tulin ilimin da GAmbari ke da shi ba ne, a’a sai don irin halayensa. Cikin yanayi na murna, ‘yan Nijeriya sun yi amanna cewa a irin wannan yanayin Shugaban Kasa na bukatar masana irinsu Gambari domin fito da kimar gwamnatin nan a ciki da wajen Nijeriya.

Farfesa Gambri na da mutunci a idon al’umman gida Nijeriya da kasashen duniya. Gudummawar da ya bayar wurin bunkasa da gina Nijeriya ba zai misaltu ba. Fiye da kowa, Farfesa Gambari ya byar da gudummawa sosai wurin sauya yanayin siyasa da bunkasar Nijeriya. Wannan ya isa ya nuna dalilin da ya sa ‘yan Nijeriya suka cika da murna da nada shi a matsayin Shugaban Ma’aikatan Buhari.

Ire-irenmu wadanda suka san Farfesa Gambari da dadewa, mun san cewa kwararren masanin Diflomasiyya ne wanda muke kiransa da ‘Bba Oba Biolorun Kosi’, ma’ana ‘Baba Babu Sarki sama da Allah’.

Abubuwa uku da za su taimakawa Farfesa Gambari wurin gudanar da aikinsa cikin sauki sune dabi’arsa, kwarewa, da kuma ilimi. A dabi’a, shugaban Kasar Amurka Abraham Lincoln ya taba cewa: “Idan kana so ka gwada dabi’ar mutum ka ba shi mulki.” Farfesa Gambari ya jima a cikin tsarin mulki a ciki da wajen Nijeriya, kuma wannan bai sa ya canza ko kadan daga dabi’arsa ba. Kamar dai yadda Lincoln ya fadi ne, shi Farfesa an bashi madafun mulki, amma ko kadan ba a taba samunsa da keta iyaka ba.

Lallai nasarar duk wani Shugaban Kasa na da alaka ne da kwarewar Shugaban Ma’aikatansa, saboda shi ne ke aiki babu kama hannun yaro a bayan fage don ganin ya magance matsaloli, shiga tsakani kafin a gabatar da su a gaban Shugaban Kasa. A lokuta da dama, shugabannin ma’aikata suna aiki ne a matsayin mafiya kusanci kuma mashawartan Shugaban Kasa. Wannan ne ya sa Farfesa Gambari ya fi dacewa da irin aikin.

A wurin wasu mulki shi ke kai wa ga makura, wasu kuma sun tafi akan cewa mulki shi ne ma makurar. Irinsu Farfesa Gambari sun fi ganin cewa mulki sila ne ga kai wag a makura. Daya daga cikin falsafofin rayuwarsa shi ne imanin da ya yi cewa mulki abu ne da ya kamata ya inganta rayuwar jama’a. A matsayinsa na shugaban cibiyar Savannah, ya nuna cewa dole ne a dage wurin tabbatar da ingancin tsarin mulki.

Duk da wasu sun fara korafi kan shekarunsa, tambayar da zan yi musu ita ce, Shugaban Amurka shekaranshi nawa? Rawar da shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ke takawa a wannan zamanin ya fi karfin a ba wanda bai san me yake yi ba, ko mara kwarewa. Mukami ne da ke da tasiri wurin shugabancin kasa.

Wadannan na daga cikin irin tarin abubuwan da ake bukata a tattare da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, wanda kuma hakan ke nuni da cewa ana bukatar mutum mai kwarewa, masanin alakar cikin gida da kasashen waje. Duk wadannan na daga cikin abubuwan da Farfesa Gambari ya kware a kansu.

Farfesa Gambari mutum ne mai gaskiya kuma wanda ke da rikon amana, tabbas zai kiyaye hurumin shugaban kasa Muhammadu Buhari a wannan lokaci da aminci ya yi karanci.

Ana gina amince ne ta hanyar zama kaifi daya. Anan dole ne shugaban ma’aikata ya zama mai natsuwa kuma kaifi daya a lokacin rikici. Shi shugaban ma’aikata mutum ne mai gina aminci tsakanin al’umma da shugaban kasa. Mafi girma da muhimmancin aminci shi ne wanda ke tsakanin shugaban kasa da shugaban ma’aikatansa.

Wani karin abu da ya ake bukata daga shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa akwai batun kwarewa a bangaren yin hukunci. Saboda yanke hukunci na daya daga cikin muhimman abubuwan da duk wani shugaban ma’aikata ke bukata. Ko ba komi aikin shugaban ma’aikata shi ne shiga tsakanin ma’aikata da shugaban kasa. Sau da yawa shugaban ma’aikata na bukatar ya yanke hukunci cikin gaggawa a kan wani lamurran.

A irin hidimar da ya yi wa kasarsa, lokacin yana ministan kasashen waje a tsakanin 1984 zuwa 1985, a zamanin mulkin soja na Buhari, Farfesa Gambari ya yi aiki babu kama hannun yaro. Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya nada shi a matsayin shugaban kula da sashen kasashen Afirka na wakilan Majalisar Dinkin Duniya a Darfur a shekarar 2010.

Haka kuma ya yi aiki a matsayin mai ba shugaban majalisar dinkin duniya shawara kan lamurran Iraki.  A duk wadannan ayyuka da Gambari ya yi ba a taba samunsa da rashin gaskiya ko wani laifi ba.

Shugaban rajin kare hakki dan adam na Amurka, wanda aka yi wa kisan gilla, Martin Luther King Jnr ya taba cewa; “Lokutan da ake gwada mutum ba su ne lokutan da yake cikin walwala ba, sai dai matsayarsa a lokutan da yake fuskantar kalubale da rashin tabbas.” A yadda lamurra ke tafiya, Farfesa Gambari dama ya kasanace mutum mai tsayuwa a bangaren adalci kuma bai taba watsawa ‘yan Nijeriya kasa a ido ba a lokutan da ya yi aiki a kasashen waje.

-Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).

0% Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0 %
Share.

About Author

Leave A Reply