FRSC Ta Nemi Gwamnati Ta Samar Wa Masu Hawa Keke Hanyoyi Na Musamman

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar FRSC ta shawarci gwamnatin jihohi dana tarayya da su samar wa masu amfani da kekuna wani gurbi na musamman a yayin gina hanyoyi a kasar nan.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, yin haka zai matukar rage matsalolin da ake fuskanta a zirga-zirga zai kuma rage yawan hatsurra da ake samu wanda kuma ke sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi masu dinbin yawa a kasar nan.

Mr Jonathan Owoade, shugaban hukumar a jihar Kwara ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai a Legas ranar Talata.

Ya ce, amfani da kekuna a wajen zirga-zirga nada matukar amfani, za a kuma amfana da shi a bangarorin rayuwa da dama.

A bikin ranar kekuna na duniya da aka yi ranar 7 ga watan Yuni, shugaban hukumar ya jagoranci masu hawa kekuna inda suka bi manyan hanyoyin garin Ilorin don fadakar da al’umma mahimmancin hawa kekuna ga rayuwa.

 

Share.

About Author

Leave A Reply