Gwamna Ahmadu Fintiri Ya Taya Alhaji Bamanga Tukur Murnar Cika Shekara 85

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya taya tsohon Gwamnan tsohuwar jihar Gongola kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Bamanga Tukur, murnar cika shekara 85 a duniya.

Fintiri ya taya dattijon murna ne cikin wani sakon da Sakataren watsa labaransa, Humwashi Wonosikou, ya fitar a Yola ranar Talata.

Ya bayyana Tukur a matsayin hamshakin dan kasuwa kuma gogaggen dan siyasa, wanda ya hidimtawa Nijeriya a matakai daban-daban da zuciyarsa daya.

Fintiri ya ce lokacin da Tukur ya yi shugabancin jam’iyyar PDP ya sadaukar ne don ceto jam’iyyar da kuma hada kan ‘ya’yanta.

“Ina yi wa dattijon fatan alheri yayin da ya cika shekara 85, sannan ina masa fatan jin dadi, morewa da kuma shagali.

“Ka yi kokari wajen samar wa kanka kima a tafiyar dimokuradiyya a Nijeriya,” inji Fintiri.

Gwamnan ya yi addu’ar lafiya da zaman lafiya ga Alhaji Bamanga Tukur yayin da ya ke cika shekara 85.

Ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin dan Adamawa nagri, yana mai cewa ayyukan da ya yi wa jihar da Nijeriya ba ta dadi za a manta da su ba.

 

Share.

About Author

Leave A Reply