Gwamna Masari Ya Tallafa Wa Masu Naqasa 200 Da Keken Guragu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

 

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bayar da tallafin kekunan guragu ga mutane 200 masu fama da larurar jiki a duk faxin qananan hukumomin 34 na jihar.

Gwamnan ya bayar da gudummawar ne a ranar Alhamis yayin qaddamar da Gidauniyar Matasa ta Aminu Masari a Katsina.

A cewar Masari, wannan karimcin wani vangare ne na qoqarin tavo rayukan masu naqasa a jihar.

Ya qara da cewa, ana sa ran gidauniyar za ta samar da kyakkyawar dama ga matasa da kuma samar da ayyukan jin qai ga marasa qarfi.

Gwamnan ya ci gaba da bayanin cewa, gidauniyar za ta fara shirin koyar da matasa don fahimtar abubuwan da suke da su da kuma kai wa ga marasa qarfi magani.

Masari ya qara da cewa, qaddamarwar ya nuna wata alama ce ta sake bayyana daga burinsa da tsare-tsarensa na makomar matasan Nijeriya don ganin sun zama masu dogaro da kai.

“Wannan shine hangen nesa na na kafa wannan gidauniya a matsayin tawa gudummawar da nake bayarwa wajen juya aqalar matasan mu daga dogaro da mutane masu qwazo da kuma fatan samun makoma mai kyau. Wannan kyautar za a yi amfani da ita ne wajen samar da tallafin da ake buqata ga matasanmu a fannonin ilimi ta hanyar ba su tallafin karatu da kuma qarfafa su,” in ji shi.

“Haka nan kuma kai wa ga kula da lafiya don ba maraxa dama da kuma kyakkyawar damar jagoranci ga matasanmu su fahimci cikakkun dabarunsu,” in ji Masari.

Ya ce, makomar matasa a Nijeriya na da nasaba da gaskiyar tattalin arzikin siyasar qasar.

Ya ce, “don haka, irin samarin da aka yiwa ado a kowace al’umma suna da alaqa kai tsaye da damar da aka basu. Matashi mai qarfin tattalin arziki zai iya kasancewa mai kishin qasa, aiki tuquru da kuma abin dogaro a qoqarin da ake na samun ci gaba mai xorewa.”

Gwamnan ya ce, “yayin da matasa ke fama da rauni ta fuskar tattalin arziki suna iya shiga cikin aikata munanan xabi’u na damfara, sata da aikata laifi iri-iri,” in ji gwamnan.

Masari ya buqaci Kwamitin Amintattu na Gidauniyar (BoT) qarqashin jagorancin Kabir Mashi da su ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da bin manufofin kafuwar.

Ya ce, kyaututtukan keken guragu mafarki ne da ya cika wa da yawa daga cikinsu saboda hakan zai kawo sauqin zirga-zirgar su.

Abubakar ya buqaci sauran masu hannu da shuni da qungiyoyi su yi koyi da gwamnan wajen kai wa ga naqasassu cikin al’umma.

bubakar ya buqaci sauran masu hannu da shuni da qungiyoyi su yi koyi da gwamnan wajen kai wa ga naqasassu cikin al’umma.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply