Gwamna Matawalle Ya Dawo Da Kwamishinoni 3 Da Ya Sauke

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da sake nada kwamishinoni 3 da kuma shugabannin wasu hukumomin gwamnatin jihar 3.

A ranar 1 ga watan Yuni ne Gwamnan jihar, ya kori sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bala Bello da dukkan kwamishinonin jihar 23 ba tare da bata lokaci ba.

Dawo da su na kunshe ne a sanarwa da Alhaji Kabiru Balarabe, mukaddashin shugaban ma’aikatan jihar ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a garin Gusau ranar Talata.

Wadanda aka dawo dasu sun hada da Alhaji Ibrahim Dosara, kwamishinan watsa labarai, Alhaji Sufyanu Yuguda, kwamishinan kudi da Hajiya Fa’ika Ahmad, kwamishinar jinkai.

Haka kuma an dawo a kwamishinan hukumar alhazai da kuma Alhaji Abubakar S/Pawa. Sauran sun kuma hada da Abubakar Sodangi, shugaban hukumar zakka da kuma Alhaji Ali Muhammad-Dama, shugaban hukumar tattara haraji na jihar.

Haka kuma Gwamnan ya dakatar da Sarkin Dansadau, Hussaini Umar, da kuma Hakimin Nasarawa Mailayi, Bello Wakkala, ya kuma umarci a gaggauta gudanar da bincike kan harkokin su .

Share.

About Author

Leave A Reply