Gwamnan Bauchi Ya Kori Kwamishinoni Da Sakataren Gwamnatinsa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya kori dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar, ciki har da sakataren gwamnati da kuma dukkan kwamishinonin jihar.

Bayanin haka yana kunshe ne a takarar da Mukhtar Gidado, jami’in watsa labarai na gwamnan ya sanya wa hannun aka kuma raba wa manema labarai a garin Bauchi ranar Laraba.

Gwamnatin ta kuma ce, rushewar ya fara aiki ne a nan take.

Gwamnan ya kuma umarci dukkan kwamishinonin su mika ragamar aiki ga babban sakataren ma’aikatar su.

Ya kuma mika godiyarsa garesu tare da kuma yi musu fatan alhairi a al’amurran da za su fuskanta a nan gaba.

Bayani yana nuna cewa, wannan rushewar ya shafi masu rike da mukaman siyasa da daman gaske.

 

Share.

About Author

Leave A Reply