Gwamnan Jihar Gombe Ya Nemi A Kara Ba Sojoji Goyon Baya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bukaci al’ummar Nijeriya su kara bayar da goyon baya ga sojojin Nijeriya don su samu nasara a kan yaki da suke yi da ‘yan ta’addan Boko Haram, da kuma ‘yan bindigar da suka addabi kasar nan.

Gwamna Yahaya ya yi wannan kiran ne a taron tunawa da mazan jiya da aka yi a babban filin wasa na Pantami da ke Gombe.

Ya ce, mazajen jiya sun bayar da rayuwarsu ga tababbatar kasar nan wadanda suke aiki kuma a halin yanzu suka fafatawa don tabbatar tsaro a fadin kasar nan kan haka ya kamata mu basu dukkan goyon bayan da suke bukata.

“A kan haka nike kira ga ‘yan Nijetiya da su cigaba da ba sojoji goyon baya da kuma karfafa su akan yakin da suke don su samu nasarar kare kasar nan daga dukkan hari da ciki da kuma wajen kasar.

“In har an basu cikkaken gudummawar da suka dace, hakan zai basu dammar fatattakar yan ta’adda a duk inda suke a fadin tarayyar kasar nan,” inji Gwamna Yahaya.

An ruwaito cewa, Gwamnan da mataimnakinsa da kuma manyan dakarun sojojin Nijeriya suka sanya furanni don karramawa tare da tunawa da mazan jiya, Gwamnan ya kuma bayar da tallafin Naira Miliyan 5 da kuma Naira Miliyan 1 na kashin kansa ga kungiyar tsofaffin sojojin don bunkasa rayuwar su.

 

Share.

About Author

Leave A Reply